✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin da ’yan Najeriya ke ciki bayan karin wa’adin canjin kudi

Akasarin masu POS a Kaduna ba su bayar da sabbin takardun kudi kuma yawancinsu suna rufe.

’Yan Najeriya sun bukaci a samar da isassun takardun sabbin kudi a bankuna domin saukaka musu halin da suke ciki na rashin sabbin kudaden.

Aminiya ta gano cewa yanzu akasarin masu POS a Kaduna ba su bayar da sabbin takardun kudi kuma yawancinsu suna rufe.

Masu kananan sana’o’i kuma na kokawa bisa karancin sabbin kudi, bankuna da rumfunan karbar kudade a ATM kuma na cike da layin mutane, duk kuwa da an kara wa’adin daina karbar tsofaffin kudaden.

Ba Mu Gamsu Da Karin Kwana 10 Ba —Sakkwatawa

A Jihar Sakkwato kuma, jama’a sun nuna rashin gamsuwarsu ga karin kwana 10 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi kan karbar tsoffin kudi.

Al’ummar sun ce akwai matsala a cikin tsarin kuma abu ne da ya kamata a duba matsalar.

Usman Aliyu, wanda Aminiya ta zanta da shi a kan titin Ahmadu Bello da ke Kaduna bayan ya fito daga wani banki ya bayyana cewa karin wa’adin da aka yi na daina karbar tsaffin kudaden ba shi ne matsalarsu ba, a wadatar da su da sabbin takardun kudaden a cikin al’umma ne ya fi.

 

“Ni a wurina kara sati babu abin da zai canza, domin a cikin banki ba su bayar da sabbin har yanzu; A ATM Kuma sai ka kwashe sa’a daya zuwa biyu kafin ka samu cire 20,000.

 

“Ka ga an takura wa jama’a, gaskiya duk yadda kake bukatar kudi a ce ba za ka iya samun sama da N20,000 ba a rana an shiga hakkin mutane,” inji shi.

 

Ya kara da cewa, “Karin wa’adin ba shi ne matsalar ba amma rashin wadata mutane da kudin ne matsalar. Da a ce a kan kanta a cikin banki za a baka damar cirar kudi yadda kake so zai taimaka.

 

“A yanzu muna tare da wasu a cikin banki suna bukatar kudi domin biyan ma’aikatansu albashi amma an ce wai ya yi transfer ya ce shi akwai mutanen da a hannunsu yake biyansu alawus.

 

“Gaskiya in dai da dama a bai wa mutane damar cirar kudi a cikin banki, ko da yake karin wa’adin abu ne mai kyau amma samar da kudin a wadace zai fi.

 

“In ba haka ba kuwa wahalar da aka Sha a baya zai Fi Wanda za’a Sha Nan da kwanaki goma masu zuwa domin a yanzu babu kudin’ inji shi.

 

Ya ce a yanzu masu P.O.S ba su da kudin da za su bayar kenan Babu kudi a banki Kuma babu a P.O.S sannan gashi babu network a wasu Bankuna.

 

Shi kuwa Suwidi Zakari Wanda bakanike ne a Sabuwar Panteka a Kaduna, wanda ya koka bisa yadda wasu mutane ke kin karbar tsaffin kudaden kafin a Kara kwanaki.

 

“A gaskiya wannan bai dace ba domin kusan kowa ya shiga tashin hankali, lokacin da wasu mutane ke kin karbar tsaffin kudaden a banki gaskiya kamata ya yi Shugaba Buhari ya saurari matsalar da talakawan ke sha saboda wannan tsari.

 

“Ni fa duk inda na je dole ma mutum ya karbi tsoffin a hannuna tunda dai babu sabbin a wadace a cikin al’umma,” inji shi.

 

Ibrahim Bashir mazaunin Sabon Garin Tudun Wada ya roki manajojin banki da su ji tsoron Allah wajen tabbatar da suna saka kudaden da suka karbo daga bankin CBN domin mutane su samu.

 

“Ya ce irin labarin da ake ji cewa wasu manajojin banki na daukar sabbin kudaden suna baiwa Yan Siyasa abin bakin ciki be. Dan haka akwai bukatar a rika cika ATM da sabbin kudaden domin saukakawa mutane Dake zuwa cirar kudi,” inji shi.

Za mu kara matsa wa CBN lamba —Wamakko

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya nuna rashin gamsuwarsa da karin kwana 10 da CBN ya kara na daina karbar tsoffin kudi a fadin Najeriya.

Sanata Wamakko wanda tsohon gwamnan Jihar Sakkwato ne ya ce kwanakin da CBN ya kara sun yi kadan don haka za su cigaba da gwagwarmaya har sai talaka ya samu sauki a Najeriya.

Halin Sakkwatawa suka shiga

Wani mazaunin garin Sakkwato, Muhammad Sani, ya ce lokacin bai wadatu ba domin mutane na cikin damuwa.

Ya ce duk da hakan dai karin yana da amfani, amma mutane na kokawa cewa sabbin kudin sun yi karanci.

“Ya kamata gwamnati ta duba koken jama’a don sun fita hayyacinsu duk da bai kamata su daina karbar tsoffin kudi ba tun da hukuma ba ta ce a daina ba.”

Bello Sani Wase, malami a makarantar koyon aikin jinya ta Jami’ar Danfodiyo, ya ce “Lura da abin da ke tafiya CBN ya tabbatar da a cikin kashi 100 na tsoffin kudi an samu mai da kashi 70.

“An yi wannan tsarin ne don amfanin kanmu da CBN.

“Ga shi har yanzu ba a daina karbar kudin ba amma abubuwa sun yi tsada an karawa mutane matsi.

Ragin cunkoson jama’a

“Karin ya kawo ragin cunkoso a banki, sai dai akwai bukatar wadatar da mutane da kananan kudin da ba a canja ba don saukakawa mutane, malamai sun yi kira da fatar za a duba, domin mutan arewa sun fi wahala da tsarin.”

Ya yi kira ga jama’a su daina kasuwancin boye kudi ka ga mutum yana da miliyan biyar yafi son ya yi matashin kai da su a gida ko ya saye kaya ya boye sai an shiga wahala ya fitar, in kudi ba su shiga baki ba, tattalin arziki ba zai bunkasa ba.

“Ina ganin ya kamata a kara in gwamnati ta ga yiwuwar haka, sai dai gwamnati ta saki kudi don mu yankin arewa mun saba da ciniki da kudi don wasu na kallon ‘transfer’ a matsayin yaudara da cuta, akwai bukatar wayar da kai samar da nasara ga tsarin.”

Kabiru Nura ya ce matsalar da ke akwai ba a fahimci tsarin ba har yanzu, domin manufar CBN takaita yawan kudi hannun jama’a, amma su mutane na kallon canjin kudi ne kawai aka yi, abin da ke kan CBN ya wayar da kan mutane kan nanufarsa ba wai karin wasu kwanakki ba.