✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Halin da na shiga bayan IPOB ta kashe matata da ’ya’ya 4’

Magidancin da IPOB ta kashe matarsa mai ciki tare da ’ya’yanta a Jihar Anambra, ya ce gwamnati ba ta ce mishi uffan ba.

Mijin Harira Ahmad, matar nan mai tsohon ciki da kungiyar IPOB ta kashe tare da ’ya’yansu hudu a Jihar Anambra, ya ce gwamnati ba ta ce mishi uffan kan abin da ya faru ba.

Malam Ahmed Jibir, wanda ke aikin gadi a wani gida, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan IPOB sun kashe matar tasa mai tsohon ciki wata tara, haihuwa yau ko gobe, ne a lokacin da take dawowa daga ziyarar da suka kai wa kanwarsa a wata unguwa.

“A garin dawowan ne wadannan suka gan su suka tare su, saboda sun gan su da Khimar (hijabi), suka harbe su gaba daya,” inji Malam Jibril Ahmad, dan asalin Karamar Hukumar Ganye ta Jihar Adamawa.

Ya ce an kashe matarsa Harira ne a yayin da suke jiran za ta haihu nan da mako guda mai zuwa.

An kuma kashe babbar ’yarsa mai suna Fatim Jibril, da kannenta mata uku; Khadija da Aziza da kuma Zaituna, mai shekara biyu.

“Yanzu haka ina jin zafi yanzu haka da nake magana da kai; gaskiya ya kamata gwamnati ta taimaka, domin yanzu haka ina cikin tsaka mai wuya,” inji Malam Jibril.

Ya ce daga bangaren gwamnati, “Ba wanda ya yi min magana… ba su ce min komai ba; ’yan sanda ne suka dauki gawar matata suka kai asibiti.

“Sun taimaka sun ba mu takarda; mun je dakin ajiyar gawa, sun ce sai na biya N30,000,’’ kafin a ba shi gawar iyalan nasa.

Sarkin Hausawa na yankin, Sa’idu Usman, ya ce kashe-kashen da IPOB take yi a yankin ya fi kamari.

Ya bayyana wa kilinmu cewa shi kansa, an kashe kaninsa a irin wadannan hare-hare.

Ya ce a cikin wata biyu da suka wuce, ’yan Arewan da aka kashe suna da yawa; “Ya faru da Barnabaz ya faru da kanina uwa daya uba daya, Amiru.