✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin da daliban Najeriya da suka makale a Sudan suke ci

Gwamnatin Tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta faro kwaso daliban Najeriya da suka makale a yakin Sudan

Daliban Najeriya da suka makale a kasar Sudan bayan barkewar yaki a can sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta taimaka ta gaggauta kwashe su.

A bidiyon wata daga cikin daliban mai suna Fauziyya, ta ce daga barkewar yakin, wanda ya yi kamari a birnin Khartoum ranar Karamar Sallah, kasashe da dama sun kwashe dalibansu daga Sudan, amma daliban Najeriya na cikin halin rashin tabbas.

A bidiyon Fauziyya wanda ya karade kafofin sada zumunta, ta ce hatta daliban kasar “Malawi da ba su da ofishin jakadanci [a Sudan] an zo an dauke su, an dauki kowa sai mu kadai a Khartoum… kowa ya gudu sai mu.”

Tuni dai kasashen duniya ke ta janye jami’an jakadancinsu daga Khartoum, bayan kazancewan rikicin shugabancin na Sudan, wanda ya yi ajalin akalla mutum 200, baya ga wadanda aka jikkata da wadanda aka raba da gidajensu.

Fauziyya, wadda ta ce kudi da ruwan sha da abincin wasu daga cikinsu ya kare, ta kara da cewa kafin wayewar garin Lahadi an fara katse katse layukan sadarwa a sassan Khartoum.

Ta ce, katse layukan sadarwar na iya sa, “Ko an zo daukar mu ba za a same mu ba. Jiya da dare wasu (dalibai) na min magana da Khartoum cewa wuta ta dauke, ba su da abinci, ba su da ruwa.

“Idan an dauke network ta yaya za a yi a ce su zo taho inda za a ce mu hadu? Dole sai an bar wasu a baya. Don Allah a yi abin da za a yi…. Yanzu ma yaya ake ciki ballantana a dauke network?” in ji Fauziyya, cikin hawaye da matukar kaduwa.

Ta ce ita da wasu dalibai shida sun isa kan iyakar Sudan da kasar Habasha, watakila su samu izinin tsallakawa zuwa kasar Habasha, amma akwai daliban Najeriya da dama a Sudan wadanda wa’adin fasfo dinsu ya kare, wasu kuma fasfo dinsu sun kone a ofishin imigireshan da suka kai domin a sabunta musu.

Don haka ta yi roko da a yi duk abin da za a yi domin a kwaso su zuwa gida kamar yadda sauran kasashe suka yi wa dalibansu.

Wannan bayani na Fauziya kuma, ba zai rasa nasaba da bayanin Gwamnatin Tarayya cewa kwaso daliban da suka kamale a Sudan zai yi wuya a halin rikicin da ake ciki ba; Amma ta kafa kwamitin kwaso su.

Sai dai a ranar Lahadi, kungiyar Daliban Najeriya da ke Sudan ta fitar da wata sanarwa da ke kira gare su da su hadu a Jami’ar Ifriqiyya ko Jami’ar El-razi ko ofishin kungiyar, domin a kwashe su zuwa kasar Habasha.

Kazalika, Shugaba Buhari ya bukaci daliban da suka makale su kwantar da hankalinsu, su kuma zauna cikin gida, yayin da gwamnati ke kokarin turawa a kwaso su.

Buhari ta hannun kakakinsa, Garba Shehu, ta ce, tana aiki haikan da ofisoshin jakadancin kasashen Sudan da Habasha, domin ganin an kwaso daliban cikin aminci.

Sanarwar da Garba Shehu ya fitar ta ce, “Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama, wanda ke kula da hakan, ya bayyana kwarin gwiwia cewa nan ba da jimawa ba za a fara kwaso daliban.”