✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji 2023: Saudiyya gano motoci 69,663 dauke da maniyyatan bogi

An tsare mazauna Saudiyya 2,000 kan yunkurin gudanar da aikin Hajji ta barauniyar hanya

Hukumomin tsaron kasar Saudiyya sun sanar da tisa keyar motoci 69,663 dauke da mutane ba bisa ka’ida ba a lokacin aikin Hajji.

Rundunar Tsaro Mai Ba da Kariya ga Alhazai ta Saudiyya ta ce jami’anta sun yi nasarar cafke maniyyata 2,062 mazauna kasar da ke kokarin gudanar da aikin Hajji ta bayan fage.

Kwamandan rundunar ya ce, “Mun kuma tsare wasu mutum 99,792 mazauna Saudiyya da suka shiga birnin Makkah ba bisa ka’ida ba.”

“Mun kuma tisa keyar motoci 69,663 da suka dauko mutane ba tare da izinin ba,” inji shi a ranar Litinin.

Hakan na zuwa ne a yayin da maniyyata daga sassan duniya ke ta tururuwa zuwa kasar domin fara gudanar da aikin Hajji daga ranar Alhamis.

Rundunar ta sanar cewa ba za ta raga wa duk wani yunkurin tayar da hankali a lokacin aikin Hajji ba.

Ta ce ta riga ta fara sanya shingaye gami da gudanar da sintiri a harabar Masallacin Harami domin cafke masu kunnen kashi.

“Kawo yanzu muna tsare da mutum 288, ’yan asalin kasar Saudiyya da mazauna kasar, kan karya dokokin aikin Hajji.

“An kuma kwace tallace tallacan bogi kan aikin Hajji guda 69, kowanne kuma an hukunta masu shi daidai da abin da doka ta tanadar,” inji sanarwar.