✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gyaran Tsarin Mulki: Yadda Aisha Buhari ta ‘kasa’ fitar wa mata kitse a wuta

Duk da zuwan Aisha Buhari Majalisar Dokoki, 'yan majalisa sun yi fatali da kudurorin mata.

Har yanzu mata masu fafutuka a Najeriya, da ma sauran ’yan kasa da ke sa ido a kan al’amuran yau da kullum, ba su gama wartsakewa ba daga kayen da wasu kudurori suka sha a Majalisar Dokoki ta Kasa a yunkurin gyaran Kundin Tsarin Mulki.

Idan ba a manta ba, kudurori biyar ne wadanda kai-tsaye za su shafi mata ’yan majalisa suka yi fatali da su, duk kuwa da ziyarar da Uwargidan Shugaban Kasa da Uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa, Aisha Buhari da Dolapo Osinbajo suka kai zaurukan Majalisar ana tsaka da aiki a kan gyare-gyaren.

A wata sanarwa da ta fitar tana nuna takaicinta bayan faruwar lamarin, Hajiya Aisha ta ce ta yi amanna Majalisar za ta iya lashe aman da ta yi, ko da yake masana harkar gyaran Tsarin Mulki sun ce bakin alkalami ya riga ya bushe.

“Shawarar da Majalisar Dokoki ta Kasa ta yanke ta yin biris da kiraye-kirayen da aka dade ana yi da a bai wa mata dama a Najeriya ta saba da fatan ’yan Najeriya masu hangen nesa maza da mata.

“Don haka akwai hujja a fushin da ’yan Najeriya suka bayyana a daidai wannan lokaci, musamman ma ganin ko a batu daya tak ba a yi wa mata rangwame ba, lamarin da ya saba da halin cude-ni-in-cude-ka da aka san majalisun dokoki na duniya da shi”, inji ta.

Kumfar baki

Tun bayan faruwar wannan lamari mata suke ta kumfar baki, har ma wasu kungiyoyinsu suka yi wa ginin Majalisar Dokokin tsinke suna zanga-zanga.

’Yar majalisar da ta jagoranci gabatar da kudurin samar wa mata kujeru 111 na musamman a Majalisar Dokoki ta Kasa (37 a Majalisar Dattawa, 74 a Majalisar Wakilai), Mataimakiyar Babban Mai Tsawatar wa Majalisar Wakilai Nkiruka Onyejiocha, ta bayyana bacin ranta ga manema labarai.

“Mazan nan sun kai mu kasa sannan sun makure mana wuya da gwiwoyinsu; ina ganin abin ya ishe su haka – amma muna jira mu ga me zai faru.

“Matan Najeriya suna jira [’yan majalisar] su fada mana dalilansu, domin na bincika ban ga wani kwakkwaran dalili ba”, inji ta.

Wata mai fafutukar kare hakkin mata, kuma shugabar kungiyar WILI mai fafutukar kai mata ga madafun iko, Maryam Baba Mohammed, ta bayyana lamarin da cewa koma-baya ne ga dimokuradiyya.

“Mu wannan ya nuna mana cewar an datse muryar mu ne; har yau namiji ba ya so ya ji muryar mace”, inji ta.

Har yanzu dai abin da mutane da dama suka bi sawun Honorebul Nkiruka suna tambaya a kai shi ne: me ya sa aka yi watsi da wadannan kudurori guda biyar?

Akwai dai amsoshi da dalilai da hasashe daban-daban da ake yadawa a kan wannan lamari.

Ranar fafe gora

Wasu na ganin cewa Uwargida Aisha Buhari da Uwargida Dolapo Osinbajo da ma daukacin masu sha’awar ganin an amince da wadannan kudurori ba su bi shawarar nan ta masu iya magana ba da suke cewa, “Ba a fafe gora ranar tafiya”.

Da yake tsokaci a kan dalilin faduwar kudurorin, mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya ce Aisha da Dolapo da ma kungiyoyin matan da suka yi zanga-zanga ba su yi kamun kafa yadda ya kamata ba.

“Amma fa dole ne mu ce an yi wannan kamun kafa a makare.

“E, ina so na ce wannan kamun kafar da neman goyon bayan kamata ya yi a ce an fara su tun tuni.

“Ba a kamun kafa kwana biyu kafin a kada kuri’a a kan muhimmin batu irin wannan; ya fi karfin kamun kafa a lokacin da aski ya zo gaban goshi”, inji shi.

Honorebul Kalu ya kara da cewa, “Ana bukatar wayar da kai sosai da sosai don gamsar da mutane su goyi bayan wannan muhimmin lamari; kun san dalili?

“Dalili shi ne ba zai yiwu ka yi shakulatin bangaro da wasu batutuwan da sabon-yankan-rake a harkar dimokuradiyya ke fama da su ba, wato tasirin addini da al’ada”.

Fushin manya?

Sai dai wasu majiyoyi a Majalisar Dattawa sun ce sanatoci sun yi wa kudurorin biyar kwaf daya ne saboda suna jin cewa fara zuwa Majalisar Wakilai da Aisha Buhari ta yi kamar rashin girmamawa ne a gare su.

Sannan Dolapo Osinbajo ta kara wa wuta fetur kasancewar ko Majalisar Dattawan ma ba ta je ba, don haka sanatocin suka ce, “Ku je kwa gani”.

Sai dai wakilin Daily Trust a Majalisar Dattawan ya ce shi bai ji wasu rade-radi game da haka ba; hujjar da mai magana da yawun Majalisar Wakilai ya bayar ita ce dahir.

Shi dai Honorebul Kalu ya ambaci addini da al’ada, wadanda ya ce suna taka rawa a rayuwar al’umma, don haka akwai bukatar aiki ja don fahimtar da mutane.

Haka kuma akwai rade-raden da ake yi cewa ’yan majalisa daga Arewa ne suka yi wa wadannan kudurori kafar ungulu.

Dalilinsu kuwa, inji wadanda suka ruwaito hakan, shi ne mata da rike gida aka san su, ba rike mukamai a majalisun dokoki, ko a gwamnati, ko a jam’iyyun siyasa ba.

’Yan Arewa

Idan ba a manta ba a shekarun baya wani dan majalisa daga Jihar Jigawa, Honarebul Gudaji Kazaure, ya taba furta irin wannan ra’ayin lokacin da ya tashi a zauren majalisar ya yi gargadin cewa tuni mata suna da cikakken iko a wasu bangarori na rayuwa, idan aka ba su wasu kujeru a gwamnati to za su mamaye komai.

Sai dai Honorebul Nkiruka ta yi fatali da zargin cewa ’yan majalisa ’yan Arewa ne suka kada kudurorin, tana mai cewa ta san wadanda suka kada kuri’ar amincewa a Majalisar Wakilai.

“Ba abin da ya hada wannan batu da Arewa. Ana cewa ’yan Arewa ne [suka sa aka yi watsi da kudurorin]; ba gaskiya ba ne.

“’Yan Arewa wadanda suka zauna a kusa da ni sun kada kuri’ar amincewa da wakilcin mata, kuma zan iya ambaton sunayensu….

“Saboda haka kada wani ya yaudare mu ya ce Arewa ce. Ba batun Arewa ba ne; batu ne na wadansu daidaikun mutane da ba sa so a dama da mata saboda wasu dalilai da su kadai suka sani”, inji ta.

Ina matan da ke majalisa?

Mai yiwuwa wani ya ce to ina matan da suke Majalisar Dokokin, me suka tabuka?

Amsa a nan dai ita ce ba su da yawa. Kai, ba a taba samun karancin mata a Majalisar Dokoki ta Kasa kamar wannan karon ba, tun 1999.

A yanzu dai mata bakwai ne a Majalisar Dattawa, yayin da a Majalisar Wakilai ake da mata 13.

Wata matsalar kuma, a cewar wasu majiyoyi, ita ce “galibin matan da ke majalisun biyu na Tarayya ’yan dumama kujera” ne, saboda ba kasafai sukan yi ma magana a zauren majalisa ba, balle har su kare wani muradi.

Hasali ma, saboda yadda wasu daga cikin matan kan bi ra’ayin maza yayin muhawara, wasu kungiyoyin kare hakkin mata na ganin su ma “maza ne”.

“Misali”, a cewar wata majiya, “akwai lokacin da aka gabatar da wani batu da ya shafi mata, sanatoci maza suka yi fatali da shi saboda wata tawaya da suka ce kudurin yana da ita.

“Wacce ta gabatar da batun ta bukaci a yi wa kudurin karatu na gaba sannan a je jin ra’ayin jama’a – a nan za a magance tawayar, amma sanatocin suka ki.

“Abin mamaki sai wata daga cikin sanatoci mata ta mike ta goyi bayan mazan, ta kara da cewa sai an je an sake aiki a kan kudurin kafin a saurare shi. Wannan ya bai wa kowa mamaki”.

Kamun kafa

’Yan majalisa dai, ta bakin Honorebul Kalu, sun ce rashin kamun kafa (abin da ake kira lobbying) ne ya sa wadannan kudurori suka kasa kaiwa gaci.

Galibi dai a tsari irin na dimokuradiyya duk wanda yake da wani muradi da yake bukatar a yi doka a kansa, yakan yi kamun kafa ne – wato ya yi ta bibiyar ’yan majalisa don ya gamsar da su muhimmancin batun.

Bayan haka kuma, su kama kafa da mutanen da suka san dan majalisa na girmama su don su saka baki.

Wannan shi ne abin da matan ba su yi ba, kuma ko lokacin da Aisha Buhari da Dolapo Osinbajo suka je majalisa, aikin gama ya gama, a cewar wasu masu ruwa da tsaki.

Amma, a cewar wasu wadanda suke da cikakken bayani game da lamarin, an kama kafa, an yi bibiya, an yi duk abin da ya kamata a yi.

Hasali ma don ganin kudurorin sun samu karbuwa a Majalisar Wakilai, tun watan Afrilun 2021 Honorebul Nkiruka ta fara kokarin gamsar da abokan aikinta don su dauki wadannan batutuwa tamkar nasu.

Kuma a cewar wasu majiyoyi, har zuwa lokacin kada kuri’a akwai alamun za a yi nasara.

“Wanne irin kamun kafa ne”, inji Maryam Baba Mohammed, “ya wuce wanda Matar Shugaban Kasa ta [yi da ta] je ta zauna lokacin da ake tara kudurorin?

“Sannan kuma Matar Mataimakin Shugaban Kasa da Ministar Mata suka je suka zauna a lokacin  da ake kada kuri’a, ko darajarsu [’yan majalisar] ba su gani ba.

“Su fada mana wanne irin ‘kamun kafa’ suke so mata su yi?”

Dan da kyar

Sai dai kuma ba a rasa komai ba, ko da kuwa bai taka kara ya karya ba, domin a Majlisar Wakilai an samu kuduri daya ya ketare siradi da kyar da jibin goshi.

Wasu rahotanni dai sun nuna cewa a Majalisar Wakilan, lokacin da aka ambaci kudiri na karshe a cikin biyar din da mata ke da muradi a kansu, wato wanda ya bukaci a ware wa mata wasu kujerun ministoci da kwamishinoni, ’yan majalisa sun kada kuri’ar rashin amincewa.

Nan take ’yan majalisar mata su 13 suka nuna rashin gamsuwa, lamarin da ya sa Shugaban Majalisa Femi Gbajabiamila ya tausaya musu, har ma ya sake yi wa sauran ’yan majalisa bayani a kan muhimmancin kudurin.

Duk da haka, kudurin ya sake shan kasa; amma sai Mista Gabajabiamila ya yi wata dabara ya ce na’ura ta lalace, a sake kada kuri’a ta hanyar cewa “E” ko “A’a”.

Sannan kuma duk da muryoyin da suke ce “A’a” sun fi yawa, Shugaban Majalisar ya buga gudumarsa ya ce “Wadanda suka ce ‘E’ sun yi rinjaye”.

Saura da me, har zuwa wani lokaci dai mata masu fafutuka za su ci gaba da korafi, watakila ma da Allah-wadai da wannan mataki na ’yan Majalisar Dokoki ta Tara.

A cewar Maryam Baba Mohammed, “Saboda sun saba zama a kan hakkin mata ne shi ya sa suke jira sai an [yi] ta bibiyar su….

“Suna jira mata su bi su suna yi musu bambadanci kafin su amince da kudurin da zai bai wa matan dan guntun “’yanci” – Majalisar Dokoki cibiya ce ta gwamnati ba gidajensu ba.

“Don haka ya kamata su koyi yanke shawara a matsayinsu na jami’an gwamnati ba a matsayinsu na masu gida ba”,

Wannan jawabi ya yi kama da abin da Aisha Buhari ma ta fada: “Ina kira ga Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai a matsayinsu na mazajen aure ko ubanni ko kanne ko yayu ko kakanni da su sake shawara su warware abin da suka yi saboda kada wata jama’a, musamman matansu na aure ko uwayensu ko ’ya’yansu mata ko abokan zamansu mata su fuskanci wariya ko a hana musu wata dama ta bayar da gudunmawa ga ci gaban kasa”.

Sai dai kuma watakila wannan shawara sai dai majalisa ta gaba ce za ta iya aiki da ita, domin a makon nan hankulan ’yan jam’iyyar APC a majalisar zai fi karkata ga babban taronsu na kasa; da sun gama kuma za su fara tunanin zabukan fid da gwani, daga nan kuma sai manyan zabukan 2023.

Abdullateef Salau da Balarabe Alkassim da Muideen Oladele sun taimaka wajen hada wannan rahoton.