✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnoni sun roki Buhari a ci gaba da amfani da tsoffin kudi

Gwamnonin sun roki Buhari da ya duba wahalar da talakawa ke sha.

Gwamnonin Jam’iyyar APC sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa baki a ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sabbin takardun kudi.

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne ya bayyana hakan bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa a Abuja.

Ya ce yayin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karbi sama da Naira tiriliyan biyu na tsofaffin kudi, amma iya Naira biliyan 300 kacal ya iya bugawa wanda a cewarsa hakan ba zai wadatar da mutane ba.

El-Rufai, wanda ya samu rakiyar takwaransa na Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kamata ya yi CBN ya buga akalla rabin abin da suka tara.

Ya ce gwamnonin jam’iyyar sun shaida wa shugaban kasa wawahalar da talakawa ke sha, da asar kayayyaki da ’yan kasuwa ke yi saboda rashin samun masu sayen kayansu.

Ya ba da misali da yadda masu sayar da tumatur suka je Legas da kayansu amma suka lalace saboda mutane ba su da kudin saye.

El-Rufai ya ce gwamnonin sun roki shugaban kasa da ya sake duba halin da ake ciki.

Ya kara da cewar shugaban gamayyar gwamnonin, Atiku Bagudu, ya sake ganawa da shugaban kasa shi kadai don jan hankalinsa kan bukatar janye dokar daina amfani da tsofaffin kudi.

A nasa bangaren, Gwamna Ganduje, ya ce shugaba Buhari ya yi alkawarin duba bukatarsu.