✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatocin jihohi za su samu tallafi don yafe haraji

Don rage radadin annobar COVID-19, Gwamnatocin jihohi 36 na Najeriya za su karbi dala miliyan biyu da rabi ko wacce a matsayin tallafi.

Gwamnatocin jihohi 36 na Najeriya za su karbi dala miliyan biyu da rabi ko wacce a matsayin tallafi don rage kudin haraji da suka yi ga mutane da ’yan kasuwa da nufin rage radadin da annobar COVID-19 ta haifar.

Gwamnatin Tarayya ce dai da hadin gwiwar Bankin Duniya suka ware kudin da jumlarsu ta kai Dala miliyan 90 don bai wa jihohin damar yafe harajin daga nan zuwa 31 ga watan Satumba.

Abdulrazaque Bello-Barkindo, shugaban sashen yada labarai na Kungiyar Gwamnonin Najeriya, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Lahadi, bayan wani taron intanet da jihohin suka yi da Bankin Duniya.

Kungiyar ta ce jihohin da suka rage wa mutane da ’yan kasuwa kudaden haraji a lokacin da aka bukata ne kadai za su amfana da wannan tallafin.

Bello-Barkindo ya ce an yi taron ne ranar Juma’a a karkashin shirin jihohi na tafiyar da kudade ta hanyar keke-da-keke wato (States’ Fiscal Transparency, Accountability and Sustainability [SFTAS]) da Ma’aikatar Kudi ta tarayya.

Ya ce mutane 125 daga jihohi 36 na Najeriya suka halarci taron, wadanda suka hada da kwamishinonin kudi da shugabannin Hukumomin Haraji.

“An samar da tallafin ne a karkashin wani sabon tsari na Ma’aikatar Kudi da Bankin Duniya na dala miliyan 750 na shirin kudaden keke-da-keke wato ‘States’ Fiscal Transparency, Accountability and Sustainability (SFTAS).

“Jihohin da suka cancanta a ba ko waccensu Dala miliyan biyu da rabin su ne wadanda suka bayyana yin rangwamen harajin a ranar 31 ga watan Yunin 2020 suka kuma aiwatar da shi ga mutane da ’yan kasuwa zuwa ranar 30 ga watan Satumba don rage radadin COVID-19”, inji Bello-Barkindo.

Ya kuma ce akwai tsarin da dole sai jihohin sun aiwatar kafin su karbi Dala miliyan biyu da rabin.

“Wannan ya hada da kwamishinan kudi ko shugaban ma’aikatar kula da haraji ya/ta bayyana kudirin jihar na yin rangwamen harajin da kuma dora ragin da suka yi a shafinsu na intanet da jaridu domin masu biyan haraji da dama su sani.

“Haka nan kuma gwamnatocin jihohin su tabbatar sun bai wa ma’aikatan haraji da masu karbar haraji ainihin abin da zai taimaka musu wajen rage kudi na tsawon lokacin da aka diba.”

Ya ce an kirikirar wa jihohin wannan shirin ne domin su mayar da hankali kan muhimman abubuwa biyar da suka hada da kara kwanakin biyan harajin da bai wa wadanda ake bi bashin haraji dama da cirewa ko kuma rage tara ko karin riba a lokacin da aka kara.