✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya za ta dawo da dokar kulle idan…

"Kasar nan na cikin mawuyacin hali, don haka dole mu kiyaye," inji Boss Mustapha.

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi cewar matukar mutane ba su bi dokar kariyar COVID-19 ba, to za a dawo dokar hana fita a fadin Najeriya.

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) kuma shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 na Gwamnatin Tarayya (PTF), Boss Mustapha ne yi wannan gargadi a ranar Litinin a Abuja, yayin gabatar da rahoton cutar.

A cewarsa, “Kasar nan tana cikin mawuyacin hali, don haka dole ne mu kiyaye shiga dokar kulle a karo na biyu.

“Zan so na tunatar da ku yadda wannan annoba ta kawo wa gwamnati koma baya, don haka dole ne ’yan kasa su zage damtse wajen yakar ta.

“Muna yin duk kokarin da ya kamata wajen guje wa sake fadawa dokar kulle a karo na biyu,” cewar  Mustapha.

Sannan ya ce Najeriya na ci gaba da samun tallafi daga ma’aikatu masu zaman kansu da ’yan kasuwa, da abubuwan da suka shafi yaki da cutar COVID-19.

An ba wa NCDC umarnin gwada mutane 348,000 a Najeriya

PTF ta ba wa Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) umarnin yi wa mutum 450 gwajin COVID-19 a kowace karamar hukuma.

“PTF ta ba wa NCDC umarnin fara yi wa mutum 450 gwajin cutar cooronavirus a fadin kananan hukumomin Najriya, kuma nan take,” inji shi.

Bayan ba da umarnin sake bude makarantu, Boss Mustapha ya ce gwamnati za ta sake yin duba game da umarnin, ganin yadda mutane ke ci gaba da kamuwa da cutar.

Ingancin allurar rigakafin COVID-19

Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 a fadin Najeriya.

Sannan ya ce gwamnati za ta tabbatar da ingancin allurar kafin fara yi wa mutane.

“Dole ne sai mun hada hannayenmu wajen fadar da mutane ingancin allurar rigakafin.

“Sannan PTF tana jadadda ci gaba da kiyaye matakan kariya daga cutar coronavirus”, inji shi.