Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan kudin makarantar ‘yan matan Chibok da ya kai kimanin Naira miliyan 164.8 a matsayin kudin zangon karatu na biyu na ‘yan matan guda 106 da Boko Haram suka sako da suke karatu a Jami’ar Amurka ta Najeriya (AUN) da ke Yola, a Jihar Adamawa.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da fadar Shugaban kasa ta fitar a karshen makon da ya gabata, wannan amincewar yana cikin alkawarin Shugaban kasa na bibbiyan halin da ‘yan matan ke ciki da kuma yadda za su dawo cikin hayyacinsu da taimaka musu wajen dawowa cikin al’umma. Sanarwar ta kuma kara da cewa shugaban, wanda ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da daukan nauyin karatun matan, ya sake nanata kudurinsa na yin duk mai yiwuwa wajen dawo da sauran ‘yan matan da suke wajen ‘yan ta’addan har yanzu.
Sanarwar ta bayar da cikakken bayanai a kan yadda aka lura da matan a lokacin da suke karkashin kulawar Gwamnatin Tarayya. A lokacin da aka fara shirin, saboda tunanin yanayin lafiyarsu da tunaninsu saboda yanayin yadda suka shiga cikin rudu da rikici a lokacin da suke wajen ‘yan ta’addan, an kai matan guda 106 cibiyoyin lafiya domin a duba lafiyarsu. A wannan lokacin ne aka canja tunaninsu wanda jami’an tsaro suka jagoranta kafin aka mayar da su karkashin kulawar ma’aikatan mata, wanda aka ba aikin lura da canja tunanin matan da kuma yadda za a dawo da su kamar yadda suke a da. Kafin sako ‘yan matan, Gwamnatin Tarayya ta bude kujera ta musamman na ‘yan matan Chibok a ma’aikatan mata, wanda zai rika kula da harkokin da suka shafi ‘yan matan, da kuma aikin bayar da bayanai da zama na tsakiya tsakanin gwamnati da wasu hukomomi da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki a lamarin.
Ma’aikatan ta mata tare da hadin gwiwar Hukumar UNFPA, da matan UN da wadansu masu bayar da tallafi, sun aiwatar da wasu shirye-shirye na musamman domin gyara tunanin ‘yan matan da kuma taimaka musu wajen dawo cikin al’umma. Wani dakin dalibai a cibiyar samar da cigaban mata, aka mayar wajen zaman ‘yan matan, inda suka zauna na wata tara. Shirin wanda aka fara a watan Janairun bana, ya kare ne a watan Satumba na bana. Kuma a lokacin aiwatar da shirin, an koyar da ‘yan matan 106 darussan lissafi, Ingilishi, Biology, Agriculture, Ilimin kimiyyar Komfuta, da sana’o’in hannu. Sannan kuma an ba su magungunan gyara tunani na musamman, da kuma shawarwari na musamman domin taimaka musu wajen mance radadin da suka shiga a baya, sanna kuma an tunatar da su koyarwar addinai, da kuma kiwon lafiya na musamman, inda aka dauko musu likitoci guda biyu da nas guda biyu. Hakanan kuma ma’aikatan ta shirya yadda iyayen matan suke zuwa ziyartarsu lokaci bayan lokaci domin suka gana da juna.
Bayan an kammala shirin cikin tsari a watan Satumba, sannan an samu cigaba sosai a harkar karatunsu, sai aka kai su Jami’ar AUN da ke Yola domin su ciga da karatu. Shigar da ‘yan matan suka yi Jami’ar AUN, shi ya fara nuna yadda ‘yan matan suke shiga cikin mutane masu yawa, wanda hakan ya cika alkawarin da Shugaban kasa Buhari ya dauka na samar wa matan ilimi mai inganci. Sanarwar ta kara da cewa, duk da cewa an mayar da su wajen iyayensu, “Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da daukan dawainiyar kudin makarantarsu har su kammala karatunsu.”