✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe duk iyakokin kan tudu

Za a rufe kan iyakokin ne daga ranar Asabar.

Yayin da ’yan Najeriya ke shirin gudanar da zabukan Shugaban kasa da na ‘yan Majalisar Tarayya a ranar Asabar, Gwamnatin Tarayyar ta ba da umarnin rufe dukkan iyakokin kan tudu na kasar.

Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, NIS, Isah Idris Jere shi ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fitar da Yammacin Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Shugaban NIS ya ce za a rufe kan iyakokin ne daga ranar Asabar zuwa Lahadi.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe duk iyakokin kasa daga karfe 12 na safiya a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023 zuwa karfe 12 na safiya a ranar Lahadi, 26 ga watan Fabrairun shekarar 2023.

“A don haka sanarwar ta ce, duk wani kwamanda ma’aikatar musamman wadanda ke jihohin da ke kan iyaka su tabbatar da ganin an bi umarnin daidai-wa-deda.”