✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta sayar da cibiyoyin lafiya na tarayya —TUC

TUC ta yi Allah wadai da yunkurin Gwamnatin Tarayya na sayar da asibitoci da kamfanin samar da wutar lantarki

Gamayyar Kungiyoyin Ma’aikata ta Najeriya (TUC) ta yi tir da shirin gwamnati na cefanar da cibiyoyin lafiya na tarayya ga ’yan kasuwa.

Kungiyar ta ce shirin gwamnati na sayar da cibiyoyin lifiya da kuma Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ba zai amfani ’yan Najeriya da komai ba.

Shugaban TUC na Kasa, Festus Osifo, ya ce “Babu amfanin da hakan zai yi idan aka yi la’akari da abubuwan da suka faru a baya, musamman cefanar da bangaren lantarki.”

Ya ci gaba da cewa, “TUC ba za ta lamunta ba, muna kuma kyamar yunkurin saboda babu amfanin da cefanar da kamfanonin gwamnati da aka yi a baya ya yi wa kasar nan.”

Osifo ya ce don haka ya ce babu abin da zai sauya zani idan Gwamnatin Tarayya ta sayar da cibiyoyin lafiya da kamfanin samar da wutar lantarki kamar yadda take shiri.

Ya bayyana haka ne a ganawarsa da manema labaria bayan babban babban taron bai-daya na kwamitocin shugabancin TUC a Abuja ranar Juma’a.

Yajin aikin ASUU

Gane da yajin aikin malaman jami’a kuwa, Osifo ya bukaci Gwamnatin Tarayya da bayar da muhimmancin da ya dace ga bangaren ilimi.

Ya ce, “Irin yadda gwamanti ta dauki bangaren ilimi ne ya sa Najeriya ta tsinci kanta a halin da take ciki yanzu.”

Amma duk da haka, “Za mu yi duk mai yiwuwa domin tattaunawa da gwamnati da kuma ASUU domin samu daidaito,” in ji shi.

A cewarsa ya kamata gwamnati ta daina biyan kudin tallafin mai domin ba shi da wani amfani saboda talakawa ba sa amfana da shi.

Maimakon biyan tallafin, gara ta yi amafni da kudin wajen biyan bukatun ma’aikatan jami’an domin su dawo bakin aikinsu.

Osifo, ya kuma bukaci gwamanti da ta dauki matakan da suka dace na gaggawa domin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar kasar nan.

Ya kuma yi tir da Naira biliyan 1.4 da Gwamnatin Tarayya ta ware domin saya wa kasar Jamhuriyar Nijar motoci.