✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta raba wa matasa rancen biliyan 75

Matasan Najeriya miliyan 68 masu shekara 18 zuwa 35 za su samu rancen domin yin kasuwanci.

Gwamnatin Tarayya ta fitar da Naira biliyan 75 don bai wa matasa bashin dogaro da kai.

Ministan Matasa da Wasannin, Sunday Dare ya bayyana haka a jawabin da ya yi wa ‘yan jarida a fadar shugaban kasa, ranar Laraba.

Dare ya ce, an kirkiri Bankin Matasa da zai taimaka wajen wayar da matasan Najeriya miliyan 68 masu shekara 18 zuwa 35 a kan harkar kasuwanci.

Ya kuma shawarci matasan da suke da tunanin wani kasuwanci da su tuntubi kananan bankuna da ke bayar da bashi guda 125 a fadin kasar nan don karbar jari ga wadanda suka cancanta.

Dare ya bayar da tabbacin cewa za a yi adalci ga matasan wajen gudanar da shirin da za a aiwatar ta fasahar intanet.

Ya ce kowa zai iya samu ba tare da bangarancin addini ko kabilanci ba.