✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati na mana azaba da yunwa —Malaman Jami’a

ASUU na zargin an ki biyan su ne domin masta musu shiga tsarin albashi na IPPIS

Malaman Jami’a na zargin Gwamantin Tarayya ta jefa su cikin yunwa domin tursasa musu karbar tsarin albashin bai daya na IPPIS.

Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU), reshen Nsukka ta yi zargin tana mai cewa a shirye kungiyar take ta yaki duk salon kassara harkar ilimi da cigaban Najeriya.

“Kungiyar ba za ta lamunci yadda aka kakaba wa ’ya’yanta IPPIS ba aka kuma ki biyan wadanda ba su shiga ba alabashi da nufin jefa su cikin yunwa ba”, inji ta.

Shugaban reshen, Dakta Igbana Ajir, ya ce da Gwamnatin Tarayya ta ki biyan malaman jami’a na tsawon wata tara da cewa dole sai dai ta biya su ta tsarin IPPIS.

Ajir ya ce, “Kin gwamanti ta karbi tsarin biyan albashi na UTAS da kungiyar ta kirkira ta kuma ba gawamnatin kyauta abin damuwa ne.

“ASUU ta sha jan hankali game da gazawa da badakalar da ke tattare da masu gudanar da IPPIS a ciki da wajen Ofishin Mai Binciken Kudi na Tarayya.

“Hanzarin da aka bayar cewa sai an gabatar da UTAS ga hukumar NITDA ta tantace ta ba da izinin amfani da shi ba tare da an sanya wa’adi ba dabara ce ta jan kafa da kuma takura wa yunkurin ASUU”.

Malaman jami’an sun bukaci gwamnati da ta nuna fahimta ta kuma sasauta wurin warware tankiyar da ta yi sanadiyar dalibai suka yi wata tara a gida.