✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Edo ya sallami kwamishinoni da hadimansa 200

Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya rushe majalisar kwamishinoni sannan ya sallami daukacikin hadimansa guda 200 har da kwamishinoni.

Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya sallami daukacikin hadimansa guda 200 har da kwamishinoni.

Sanarwar da kakakin gwamnan, Crusoe Osagie, ya fitar ta ce gwamnan ya sallami kwamishinonin tare da rushe kwamitin zartarawar jihar ne a zaman Majalisar zartarwar jihar da ya jagoranta a ranar Laraba.

Baya ga kwamishinoni, hadiman gwamnan Obaseki da aka sallama sun hada da masu ba shi shawara (SA) da kuma masu ba shi shawara na musamman.

Ya bayyana cewa duk da haka, gwamnan ya bayyana godiya ga kwamishinonin bisa yadda suka hidimta wa gwamnati da al’ummar jihar ta Edo.