✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna ta yafe wa ’yan wiwi 47,000

Za ta biya tarar Naira biliyan 109 da aka yi musu

Gwamnar Jihar Oregon da ke Amurka, Misis Kate Brown, ta sanar da yin afuwa ga mutanen jihar da kotuna suka samu da laifin mallakar tabar wiwi.

An yi afuwar ga mutanen da aka samu da laifin mallaka ko tu’ammali da abin da ya gaza kilo daya na tabar wiwi, kafin shekarar 2016 a lokacin da suke da shekara 21 ko sama da haka.

Yafewar ta shafi akalla mutum dubu 47 da 144, sannan ta ce za ta biya kudin tarar da aka yi musu ta Dala miliyan 14 (kimanin Naira biliyan 109).

A wata sanarwa da ta fitar, Gwamna Brown ta ce, “Babu wanda ya cancanci a daure shi har abada saboda an kama shi da laifin mallakar tabar wiwi, wanda laifi ne da ba ya cikin littattafan shari’a na Jihar Oregon.”

Madam Brown ta ce wannan yunkuri an yi shi ne domin “daidaita kurakuran tsarin shari’ar laifuffuka da rashin adalci a Oregon idan ana maganar mallakar tabar wiwi.”

Brown ta ce, “Bai kamata mutanen Oregon su fuskanci rashin tsaro a gidaje da rashin aikin yi, da cikas ga harkar ilimi ba, sakamakon yin wani abu da ya zama ba wata cikakkiyar doka a kansa a yanzu, kuma har su shafe wasu shekaru a gidan yari.

Don haka wannan afuwa za ta kawar da wahalhalun nan.

A cewar ofishin gwamnar, afuwar ta shafi hukuncin jiha ne kawai, saboda kundin shari’a da sashen shari’a na Oregon ke amfani da shi, ba ya da damar shiga na jihohi ko kotunan shari’a na tarayya.