✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar Maiduguri: Zulum ya ba wa ’yan kasuwa tallafin N1bn

Zulum ya karbi bakuncin daruruwan ’yan kasuwar da iftila'in gobara ya shafa

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya karbi bakuncin daruruwan ’yan kasuwar Monday Market, wadanda iftila’in gobara ya shafa.

Yawancin ’yan kasuwar, wadda ita ce mafi girma a Maiduguri, babban birnin jihar, sun rasa shagunansu da kayayyakinsu na biliyoyin Naira a gobarar da ta tashi da gabanin wayewar garin ranar Lahadi.

A lokacin da ya karbi bakuncinsu, Zulum ya ya mika musu cekin kudi na Naira biliyan daya su raba a matsayin agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa, har zuwa lokacin da kwamitin bincike zai fitar da sakamakon aikin da aka sa shi.

A cikin  jawabinsa ga al’ummar jihar a ranar Lahadi bayan ziyarar gani da ido a kasuwar, Gwamna Zulum  ya  yi alkawarin tallafin Naira biliyan daya.

Kasuwar Litinin ta Maiduguri, wadda aka ce ita ce mafi girma a yankin Arewa maso Gabas, daya ta kone kurmus sanadiyar gobarar da ta dauki tsawon wasu sa’o’i.

Shu’umar gobarar ta tashi ne tsakanin karfe 1 na safe zuwa 2 na dare, kuma zuwa yanzu ba a san musabbabin tashinta ba.

A lokacin da ya karbi bakuncin ’yan kasuwar a ranar Litinin a Maiduguri, a gidan gwamnati, Zulum ya ce, “Na Sake jajanta muku bisa bala’in gobara da ta mamaye kasuwar Litinin da ke Maiduguri baki daya.

“Yawancinku sun yi asarar dukiyoyinku, ina rokon ku da ku dauki wannan iftila’in a matsayin kaddara daga Allah Madaukakin Sarki.

“A  matsayina na gwamnanku, zan hada kai da sauran masu ruwa da tsaki wajen yin duk abin da za mu iya wajen bayar da tallafin da ake bukata ga duk wadanda abin ya shafa.

“Ina da tabbacin shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa Gwamnatin Tarayya za ta ba da hadin matuka.”

Gwamna Zulum ya sanar da wadanda abin ya shafa cewa ya nada wani mutum mai mutunci Engr.  Zarami Dungus, wanda tsohon babban sakatare ne, da zai jagoranci kwamitin da zai fara tantance wadanda abin ya shafa da kuma raba musu Naira biliyan daya.

A cewarsa, an bada wadannan  kudaden ne don bayar da tallafi cikin gaggawa ga wadanda abin ya shafa

Ya ba da umarnin cewa kwamitin ya kunshi wakilin hadin gwiwa na kasuwar, wakilin kungiyar ’yan kasuwa, da kuma wani wakilin tashar mota ta kasuwar da dai sauransu.