✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara: Ya kamata gwamnati ta tallafa wa ’yan Kasuwar Borno —Majalisa

Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa ’yan kasuwar da suka yi asara a gobarar Kasuwar Monday da ta Gamboru a Jihar Borno

Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa ’yan kasuwar da suka yi asara a gobarar Kasuwar Monday da ta Gamboru da ke Maiduguri a Jihar Borno.

Aminiya ta ruwaito cewa sama da shaguna dubu goma ne suka kone a gobarar Kasuwar Monday da ke Maiduguri ranar 26 ga watan Fabrairu; Kasuwar Monday ita ce kasuwa mafi girma a Jihar Borno da ma yankin Arewa maso Gabas.

Bayan mako uku aka yi wata gobarar a Kasuwar Gamboru, inda aka tafka asarar dukiya mai yawan gaske.

A kan haka ne majalisar ta bukaci gwamnati ta tallafa wa ’yan kasuwar da iftila’in ya shafa bayan Honorabul Abdulkadir Rahis ya gabatar da kuduri a kan hakan  a ranar Alhamis.

Rahis ya ce: “A yayin da Kasuwar Monday ce babbar cibiyar kasuwanci a Arewa maso Gabashin Najeriya da kasashe makwabta; Kasuwar Gamboru na da matukar muhimmaci ga al’ummar Maiduguri, musamman a bangaren kayan abinci.

“Gobarar ta kawo koma-baya ga miliyoyin jama’a da ke amfana da kasuwannin, don haka akwai bukatar bayar da dauki ga wadanda abin ya shafa.”

Idan ba a manta ba, bayan gobarar Kasuwar Monday, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ba wa ’yan kasuwar tallafin Naira biliyan daya.

Honorabul Rahis, ya ce duk da haka akwai bukatar Ma’aikatar Agaji da Jinkai da Hukumar Kula da Ci gaban yankin Arewa maso Gabas da Hukumar SMEDAN su agaza wa ’yan kasuwar don farfado da harkokinsu.