✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a babbar kasuwar Nguru

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga tantance musabbabin gobarar ba.

Babbar kasuwar garin Nguru da ke Karamar Hukumar Nguru a Jihar Yobe yanzu haka na can na ci da wuta.

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar ranar Asabar.

Wani ganau, Abubar Ibn Usman, wanda yanzu haka yake wajen ya ce wutar ta fara ne kimanin sa’o’i uku da suka gabata, kuma tana can tana cin sashen ’yan gwanjo na kasuwar.

A cewarsa, shaguna da wuraren ajiye kayayyaki na miliyoyin Nairori sun kone a sakamakon gobarar.

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga tantance musabbabin gobarar ba.