✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta kashe mutum 9, an ceto 72 a Kano

Hukumar kwana-kwana ta samu kiraye-kirayen gaggawa guda 49 a watan Satumba, 2022

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ceto rayuka 72 da dukiyoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 38.6 a gobara a watan Satumba.

Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya ce mutane tara ne suka rasa rayukansu a gobara 17 da ta ta lakume dukiyoyin da kimarsu ta kai Naira miliyan 14.8 da ta afku  a cikin watan.

A bayaninsa na ranar Talata a Kano, Alhaji Saminu ya ce, hukumar ta amsa kiraye-kirayen gaggawa guda 49, sannan ta samu kirayen-kirayen nema agajin karya 11 tsawon lokacin.

Ya bukaci jama’ar jihar da su kasance masu taka-tsansan da wuta sannan a i kira ga masu ababen hawa da su kiyaye dokokin hanya domin guje wa hadurra, musamman a lokacin damina.