✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniya ta karrama ma’aikacin Aminiya

Gidauniyar ta ce ta karrama shi ne saboda gudunmawarsa wajen ci gaban yankin.

Gidauniyar Amash ta karrama Editan Tace Labarai na Jaridar Aminiya, Isiyaku Muhammed saboda irin gudummawar dayake bayarwa wajen ci gaban anguwar Hayin Banki da ke Kaduna.

Gidauniya ta kuma karrama Hon. Aliyu Haruna Chakis da marigayi Malam Sa’adu Hayin Banki da marigayi Malam Shehu Umar Balarabe, da marigayi Sheikh Bello da Shugaban Kamfanin Bash Technology, Bashir Idris da Kansilan Hayin Banki, Malam Abdullahi Danladi da kuma Kwamared Ismail Galadima da sauransu.

Da yake jawabi kan dalilin karrawamar, Shugaban Gidauniyar ta Amash kuma shugaban rukunin makarantun Amash, Malam Jafar Umar Abdullahi ya ce sun karrama wadanda aka zaba bisa jajircewarsu wajen gudunmuwar da suke ba al’umma a fannoni daban-daban.

“Wannan ya sa muka karrama har da wadanda suka rasu domin nusar da wadanda suke raye.

“Mun kafa gidauniyar Amash ne domin taimakon marayu da sauran marasa karfi,” inji shi.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Sarkin Hayin Banki, Malam Mahmud Shehu Galadima, da Danmajen Hayin Banki, Malam Ibrahim Yala da Hon. Naziru Sanusi Abubakar, da Malam Ishaq Ibrahim da sauransu.