✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gbajabiamila ya taya APC murnar cin zabukan cike gurbi

Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya Femi Gbajabiamila ya taya Jam’iyyarsa ta APC murna bisa nasarar da ta samu a zabukan cike gurbi da aka gudanar…

Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya Femi Gbajabiamila ya taya Jam’iyyarsa ta APC murna bisa nasarar da ta samu a zabukan cike gurbi da aka gudanar ranar Asabar a fadin Najeriya. 

A sakon da ya aike ta bakin mashawarcinsa kan kafafen yada labarai, Lanre Lasisi a ranar Lahadi, Gbajabiamila ya ce nasarar da APC ta samu a wasu jihohi ya kara tabbatar da irin kauna da gamsuwa da mutane da wadanda da jam’iyyar ta fitar a matsayin ’yan takara a kujeru daban-daban.

Gbajabiamila ya kuma mika sakon taya murna na musanman ga APC reshen Jihar Legas bisa nasarar da ta samu a zaben cike-gurbin mazabar Legas ta Gabas da mazabar dan Majalisar Jiha mai wakiltar mazabar Kosofe II, Tokunbo Abiru da Obafemi Saheed.

Shugaban Majalisar ya kuma taya Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu bisa nasarar da jam’iyyar ta samu a karkashin jagorancinsa.

Ya bayyana cewa APC za ta ci gaba da samun nasarar lashe zabuka a ko’ina a fadin Najeriya.