✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya ziyarci ’yan uwan Kanawa 16 da suka mutu a hatsarin mota

A ranar Asabar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kai ziyara zuwa garin Dambatta na Karamar Hukumar Dambatta ta jihar, inda ya jajanta…

A ranar Asabar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kai ziyara zuwa garin Dambatta na Karamar Hukumar Dambatta ta jihar, inda ya jajanta wa ’yan uwan mutum 16 da suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Kano Abba Anwar ya fitar, ya ce gwamnan ya kuma ba da gudunmuwar kudi na Naira dubu 100 ga kowane dangin mamatan domin rage radadi.

Sanarwar ta ce, “lokacin da muka samu labarain hatsarin da ya rutsa da mutane 16 daga Karamar Hukumar Dambatta da kuma wani daga Karamar Hukumar Kura, mun kadu da lamarin sosai.”

Aminiya ta samu cewa ’yan uwan mamatan da suka fito daga yankuna daban-daban na Karamar Hukumar, sun taru a wurin guda cikin garin Dambatta inda gwamnan ya yi musu ta’aziyya cikin juyayi da yanayi na bakin ciki.

Ya tunatar da ’yan uwan mamatan cewa wannan musiba daga Allah Madaukakin Sarki ta ke, yana mai ba da shawarar cewa abin da ya rage shi ne su ci gaba da yi musu addu’a.

Daya daga cikin ’yan uwan mamata da ya wakilci sauran, Sulaiman Muhammad, ya yaba wa gwamnan bisa wannan karamci da ya nuna da damuwarsa a kan a kan abin da ya faru, “mun yi murna da cewa gwamnan yana nan tare da mu.”

Aminiya ta ruwaito cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana juyayinta kan mutuwar mutanen tare da yin karin haske dangane da musabbabin mutuwarsu

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Samuel Aruwan ya ce mutanen sun gamu da ajalinsu ne bayan tayar motarsu ta fashe a unguwar Rigachikun da ke Karamar Hukumar Igabi ta jihar.

Ya karyata labarai da ke cewa ’yan bindiga ne suka yi wa Kanawan ruwan wuta a Jihar Kaduna kan hanyar Abuja zuwa Kano.

“Gaskiyar maganar ita ce sun yi hatsari ne a hanyar Zariya zuwa Kaduna a daidai unguwar Rigacikun inda tayar motarsu ta yi bindiga”, inji Aruwan yayin ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Kano da iyalan mamatan.