✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya sanya ranar mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da Malaman Kano

Za a gudanar da mukabala domin bambance tsakanin zare da abawa.

Gwamnatin Jihar Kano ta sanya ranar Lahadi, 7 ga watan Maris na 2021 a matsayin ranar da za a gudanar da mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da Malamai a Jihar.

Kwamishinan Yada Labaran Kano, Muhammad Garba da kuma takwaransa na Ma’aikatar Harkokin Addini, Dokta Muhammad Tahar, sun tabbatar da hakan kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Makonnin baya Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya amince a kan shirya wata mukabalar ilimi tsakanin malamai da kuma Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara biyo bayan kalaman da malamin ya yi wanda ake zargi sun saba wa koyarwar addinin Islama.

Wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Jihar Kano Abba Anwar ya fitar tun a ranar 7 ga watan Fabrairu, ta ce za a shirya zaman baje kolin dalilai na ilimi inda malamai daga bangarori da dama za su gabatar da hujjojinsu dangane da goyon bayan malamin a kan akidarsa ko sabanin haka.

Sanarwar da hadimin gwamnan ya fitar ta ce nan da ’yan kwanaki kadan masu zuwa za a sanya rana da kuma wurin da za a gudanar da wannan tattaunawa wacce za a gayyato malamai domin su shaida daga ciki da wajen Jihar Kano.

Aminiya ta samu cewa sanarwar wannan mataki na zuwa ne bayan wata tattaunawa da Gwamna Ganduje ya yi tare da Kwamishinan Harkokin Ilimin Addini na Jihar Kano, Dokta Muhammad Tahar Adam da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Ali Haruna Makoda da kuma tsohon dan takarar Gwamnan Kano, Malam Salihu Sagir Takai da sauransu.

Kazalika, sanarwar ta ce Gwamnati Kano ta bayar da tabbacin samar da tsaro mai inganci a yayin mukabalar sannan ta amince a watsa ta kai tsaye a gidajen Rediyo na Jihar da na ketare.

Gwamnan ya yi kira da al’ummar Jihar da su kwantar da hankulansu a yayin mukabalar ta kuma bayanta.

Ana iya tuna cewa Gwamnatin Kano ta rufe masallacin Sheikh Abduljabbar Kabara, bisa zargin malamin da yin izgili ga Sahabban Manzon Allah (SAW).

Gwamnatin Jihar ta kuma rufe daukacin cibiyoyin karatu da majalisin Sheikh Abduljabbar, ta hana shi gabatar da wa’azi ko lakca; sannan ta dakatar da kafafen yada labarai daga sanya karatuttukansa ko hudubobi ko da’awa.