✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya ba mutumin da ya rasa iyalai 7 a gobara tallafin N3m

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da tallafin Naira miliyan uku ga mutumin da ya rasa iyalai bakwai a gobara

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan uku ga Malam Abdulrahman Ibrahim Wailari, mutumin da ya rasa iyalai bakwai a sakamon gobara domin rage radadinta.

Mutumin dai mazaunin unguwar Wailari a Karamar Hukumar Kumbotso ya rasa iyalan ne sakamakon wata gobara da ta tashi a gidansa a makon day a gabata.

Gwamnatin dai ta sanar da bayar da tallafin ne yayin bikin kaddamar da kayyakin tallafi ga iyalai 1,500 a fadin jihar.

An ba shi tallafin ne domin ya sami damar sake gina gidansa wanda gobarar ta cinye

Yayin gobarar dai, mutumin ya rasa mahaifiyarsa, ’ya’aynsa guda biyu, kanwarsa da kuma ’ya’ayanta su uku.

Rahotanni sun nuna cewa wutar ta tashi ne sakamakon wani maganin sauro da aka kunna lokacin suna tsaka da bacci.