✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane na wa gwamnoni kallon barayi —El-Rufai

Ya ce mutane na wa gwamnoni kallon masu barnata dukiyar al’umma da ba sa tsinana komai

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir Ahmed El-Rufai, ya ce ana yawan munana zato ga jami’an gwamnati ta yadda galibin mutane ke daukarsu a matsayin barayi.

Ya ce akasarin mutane suna yi wa gwamnoni kallon masu barnatar da dukiyar al’umma da ba sa tsinana komai.

“Gwamnoni su ne wadanda aka fi munana wa zato cikin dukkanin zababbun jami’an gwamnati.

“Kowa na ganin gwamnoni barayi ne kuma ba sa yin komai sai barnatar da dukiyar kasa”, inji shi.

El-Rufai ya fadi hakan ne hirar da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily na gidan talbijin na Channels a ranar Litinin,

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da yake amsa tambaya game da aiki mafi wahala da gwamna ke yi a Najeriya.