✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fiye da mutum dubu 800 za su tsere daga Sudan —MDD

Ya zuwa yanzu mutane dubu 73 ne suka rankaya kasashen da ke makwaftaka da Sudan.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu 800 ne ake sa ran za su tsere daga Sudan sakamakon kazamin rikicin da ake yi tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun Kai Daukin Gaggawa na RSF.

Wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya, Raouf Mazou ne ya bayyana hakan ranar Talata a birnin Geneva na Switzerland.

Mazou ya bayyana cewa, idan ba a warware wannan rikici da wuri ba, za a ci gaba da samun dimbin mutanen da ke arcewa daga Sudan don neman mafaka da agaji.

Saboda haka ya ce a tattaunawar da suka yi da hukumomin da wannan lamari zai shafa, sun cimma matsayar shirya wa mutane dubu 815 da ake sa ran za su iya arcewa zuwa kasashe 7 da ke makwaftaka da Sudan.

Wannan hasashe da aka yi, in ji Mazou ya hada da kimanin ’yan kasar Sudan dubu 580 da kuma wadanda ke gudun hijira a halin yanzu daga Sudan ta Kudu da wasu wuraren.

Ya zuwa yanzu, mutane dubu 73 ne suka rankaya kasashen da ke makwaftaka da Sudan da suka hada da Sudan ta Kudu, Chadi, Masar, Eritrea, Habasha, Jamhuriyar Tsakiyar Afrika da Libya.

A ranar 15 ga watan Afrilu ce rikici ya barke tsakanin rundunar sojin Sudan da ke biyayya ga jagoran mulkin sojin kasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan da dakarun kai daukin gaggawa, karkashin jagorancin Janar Hamdon Dagalo.