✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitinar Boko Haram somin tabi ce idan ISWAP ta bunkasa —Zulum

Zulum ya sake nanata kiransa ga Gwamnatin Tarayyar kasar cewa ta dauko sojojin haya daga ketare.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi gargadin cewa fitinar Boko Haram da ake fama da ita a yanzu za ta zama ‘wasan yara’ muddin aka yi sake kungiyar ISWAP ta bunkasa.

Zulum ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa ranar Alhamis a Abuja.

Da yake batu kan ci gaban da ake samu dangane da yaki da Boko Haram da kungiyar ISWAP a Arewa maso Gabashin kasar, Zulum ya nemi dakarun sojin kasar da su sauya dabarun dakile kungiyoyin ta’addan biyu da a cewarsa sun kasancewarsu babbar barazana ce ga kasa baki daya.

Gwamnan ya ce mayakan ISWAP na kara bunkasa a Jihar Borno a sakamakon kusancinta da yankin Sahel.

Kazalika, Zulum ya sake nanata kiransa ga Gwamnatin Tarayyar kasar cewa ta dauko sojojin haya daga kasashen wajen domin su taimaka mata murkushe kungiyoyin ’yan tayar da kayar baya.

Muddin ba a tashi tsaye ba, mayakan ISWAP za su fitini Najeriya —Zulum

A bayan nan ne Gwamna Zulum, ya nuna “matukar” damuwa kan yadda mayakan ISWAP ke karuwa a wasu sassan jihar, lamarin da ya sa ya yi kira da a tashi tsaye a dauki matakan gaggawa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Kwamitin Majalisar Dattawa da ke kula da sha’anin sojin kasar da ya ziyarce shi a ranar Laraba a Maiduguri.

Yayin da yake yabawa gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro bisa nasarorin da aka samu a Borno, Zulum ya ce ya damu matuka game da karuwar mayakan ISWAP a sassan jihar, musamman daga bangaren kudanci, inda ya kara da gargadin cewa bangaren na ISWAP sun fi na Boko Haram karfi da kuma makamai.

Gwamnan ya koka kan cewar idan ba a gaggauta daukar mataki ba, barzanar na iya zama illa ba ga mutanen Arewa maso Gabashin Najeriya kadai ba, har ma da kasa baki daya.

“Maganar gaskiya ita ce, ya zama dole mu dauki mataki a kan mayakan ISWAP a Jihar Borno, idan muka ki fatattakar su, ta yi wu su zama matsala ba ga yankin arewa maso gabas kadai ba, har ma da daukacin Najeriya.”

Farfesa Zulum ya kara da cewa, “mayakan ISWAP na da makamai kuma a shirye suke sannan suna da basira fiye da mayakan Boko Haram kuma suna karuwa akai-akai, dalilin kenan da ya sa ya kamata a fatattake su.”

Gwamnan ya kuma mika godiya ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da dakarun Najeriya da masu ayyukan sa-kai saboda irin taimakon da suke bayar wa.

“Jihar Borno na ganin dawowar zaman lafiya a hankali wanda hakan ya yi wu ne saboda taimako da gwamnatin tarayya ta ba mu.

“Sannan shugabannin jami’an tsaro su ma suna ba da nasu hadin kan. A takaice, shugabannin rundunonin soji su ma suna ba da nasu taimakon,” a cewar Zulum.

Sai dai gwamnan ya nuna damuwa kan yadda mayakan ISWAP suke barazanar mayar da hannun agogo baya kan nasarorin da aka samu.

A gefe guda kuma gwamnan har ila yau ya ce mika wuya da daruruwan mayakan Boko Haram suka yi a kwanan nan, ya sa ana samun zaman lafiya musamman a yankunan da ake harkokin noma.

Gabanin jawabin na gwamna Zulum, Sanata Ndume wanda ke zaman jagora ya bayyana cewa kwamitin ya kai ziyarar ne don nuna godiya ga gwamnatin jihar Borno kan yadda take ba sojoji hadin kai da taimako, batun da su ma dakarun kasar suka jaddada a baya.