Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United da Chelsea sun yi kunnen doki a Gasar Firimiyar Ingila.
Ƙungiyoyin biyu sun tashi 1-1 a wasan hamayya da suka buga da yammacin ranar Lahadi, a filin wasa na Old Trafford.
- Tinubu zai rantsar da sabbin ministoci a ranar Litinin
- Ɗan ci-ranin Arewa ya zama shugaban kamfanonin haƙar ma’adinai a Kudu
Bruno Fernandez ne ya fara jefa wa Manchester ƙwallo a minti na 70 a bugun fenariti, bayan dawowa daga hutuk rabin lokaci.
Chelsea ta warware ƙwallon a minti ma 74 ta hannun ɗan wasan tsakiyarta Moises Caisado.
Chelsea na mataki na huɗu da maki 18 daga wasa 10 da ta buga a gasar.
Manchester United kuwa na mataki na 13 ds maki 12 daga wasa 10 da buga a gasar.
Ƙungiyar Liverpool ce ke kan ragamar gasar da maki 25 daga wasanni 10 da ta buga.