✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FIFA ta amince a sake doka wasan Argentina da Brazil da ta dakatar a bara

Tun a minti na bakwai da fara wasan ne aka tayar da hargitsi.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA ta sanar da yiwuwar bai wa kasashen Brazil da Argentina damar doka wasansu na neman gurbin zuwa gasar Cin Kofin Duniya da ta dakatar a bara sakamakon takaddama kan karya dokokin yaki da cutar Coronavirus da ta kai ga rikici.

Duk da cewa kasashen 2 dukkaninsu sun samu tikitin zuwa gasar ta cin Kofin Duniya da za ta gudana a Qatar a karshen shekarar nan, amma dukkaninsu sun suna bukatar doka wasan cikin takardun da suka aikewa FIFA.

A baya dai FIFA ta yi watsi da daukaka karar da kasashen 2 suka shigar don basu damar doka wasan da kuma janye tarar da aka lafta musu ta $70,000 saboda takaddamar ta ranar 5 ga watan Satumban bara, wanda ya kai ga basu damar doka wasan a watan Fabarairu amma karkashin tsauraran sharudda da dukkaninsu suka ki amincewa.

An dai dakatar da wasan ne a wancan lokaci sakamakon shigar wasu ’yan wasan Argentina hudu, wanda hukumomin lafiyar  Brazil suka ce ba su killace kansu na tsawon kwanaki ba wanda kuma ya saba wa dokokin yaki da Covid-19.

’Yan wasa na Argentina hudu da FIFA ta kuma dakatar daga buga wasanni biyu na gaba sun hada da Cristian Romero da Giovani lo Celso da Emiliano Martinez da kuma Emiliano Buendia.

Aminiya ta ruwaito cewa, minti bakwai da fara wasan ne ma’aikatan lafiyar Brazil suka kutaa cikin filin wasan da ke birnin Sao Paolo, wanda ya kai ga an yi hargitsi tsakanin ’yan wasa da sauran ma’aikatan kasashen biyu.

Kawo yanzu dai FIFA ba ta ayyana ranar da za a fafata wasan ba.