✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fatima Maikusa: Gwarzuwar lissafi ’yar shekara 15

Fatima wadda ta lashe gasar lissafi na kasashe sau bakwai ta ce darasin ya fi sauran sauki

Fatima Adamu Maikusa ’yar shekara 15 ta zama gagara-badau inda ta lashe gasanni bakwai na lissafi a kasashe daban-daban.

Fatima wadda yanzu ta zama abin koyi ga dalibai mata, ta fara nuna bajintarta a bangaren lissafi ne tun tana ’yar shekara tara.

A zantawarta da ta Aminiya, Fatima wadda take ajin karshe na sakandare a Makarantar Tulip International (NTIC) da ke Kano, ta bayyana cewa lissafi ya fi sauran darussa sauki.

Ga yadda hirar ta kasance da Fatima Adamu Maikusa, ’yar asalin Jihar Gombe, inda ta bayyana yadda ta fara son lissafi da abin da take burin zama a nan gaba:

Za mu so ki gabatar da kanki

Sunana Fatima Adamu Maikusa, ni ce Gwarzuwar Gasar Lissafi ta Amurka (AMC 08) da Gasar lissafi ta Kasa da Kasa ta Eduversal a kasar Indonesia da Gasar Lissafi ta Kasa da Kasa a kasar Thailand da Gasar Lissafi ta Kangourou Sans Frontiers – KSF.

Ni ce kuma Gwarzuwar Gasar Olympic na Lissafi na Masu Tasowa (FISO) da Gasar Mathematics Without Borders a kasar Bulgaria sai kuma Gasar Lissafi ta Komodo a Indonesia.

Mene ne ya sa miki sha’awar darasin lissafi?

Tun daga makarantar firamare nake son lissafi, saboda yana daga cikin darussa mafiya sauki kuma ina jin dadin sa.

Yawancin dalibai na tsoron lissafi, me ya sa kika ce ya fi sauran darussa sauki?

Ka san idan ba ka iya abu ba wahalar da kai zai yi, wanda hakan zai sa abin ya rika takura maka, har ka tsane shi.

Watakila sauran daliban ba su ga daya bangaren na lissafi ba, wahalar suke gani.

Shin ana koya miki lissafi a gida ne bayan makaranta?

A’a ba ni da ko mai koya min karatu a gida.

Baiwa ce ke nan?

Gaskiya kam.

Ko dai mahaifiyarki ce take koya miki?

A’a, ba na yin wani darasi a gida bayan an taso makaranta, amma dai tun ina firamare ni da kaina ina yawan yin sa, saboda yadda nake son sa.

Yaya kika kasance a wadannan gasanni da kika lashe?

Wadansnsu na da wahala, amma mun yi nasara. Abin farin ciki ne a ce mutum ya yi wata gasa. Akwai kayatarwa

Da farko na tsorata, amma kuma kasancewar ina bukatar wadannan kambuna saboda ina son zuwa Jami’ar Harvard, kuma irin wadannan kambuna suan daga daga cikin abubuwan da ake bukata daga gare ni.

Yaya kika ji a lokacin da aka bayyana ki a matsayin wadda ta lashe gasar?

Farin ciki ya lullube ni. A lokacin da gasar take gudana na ga alamar nasara, amma ban yi tunanin ni ce zan lashe ba. Saboda haka na yi mamaki.

Su wane ne abin koyinki?

Mahaifana da malamaina sai kuma duk mutanen da suka samu nasara a rayuwa.

Me kike sha’awar ki zama a nan gaba?

Ina so in zama kwararriya a fannin manhajar kwamfuta a Jami’ar Harvard, da yardar Allah.

Me ya sa; ko dai saboda ya kunshi lissafi ne?

Kwarai, ina son lissafi. Ina son kafa tarihin kirkiro abubuwa da magance matsaloli, musamman abin bangaren da ya shafi dumamar yanayi da abubuwan da za su kawo sauki ga rayuwar dan Adam.

Me kike tunani ya taimaka miki wajen samun kwarewa a lissafi?

Daga ciki akwai horon da muka rika samu a lokacin da nake firamare da karamar sakandare.

Kasancewar ina son karantar fannin manhajar kwamfuta sai na kara dagewa na inganta ilimina ta hanyar halartar azuwan horo a bangaren na lissafi

Ina kuma godiya ga malamaina da makarantarmu saboda sun taimaka mini kwarai, suka sa na shiga ajin dana kara samun gogewa.

Sai kuma iyayena, musamman mahaifina wanda ke goyon bayan ganin cikar burina.

Yanzu haka ina shirye-shiryen neman gurbin karatu a Jami’ar Harvard kuma mahaifina ya dauke shi da muhimmanci sosai.