✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashewar tankar mai ta kona mutum 5 kurmus

Motar da ke makare da man fetur ta yi bindiga ne bayan ta fadi.

Mutum biyar sun kone kurmus, wasu biyu kuma suka ji rauni a lokacin da wata tankar mai ta yi bindiga a ranar Laraba.

Lamarin ya faru ne bayan tankar ta fadi a kan hanyar Ajilete da ke kan titin Owode-Idiroko a Jihar Ogun.

  1. Mun gano Ministar da ta sayi kadarar Dala miliyan 37 a boye — EFCC
  2. Yadda Fani-Kayode ya hada ni da Nnamdi Kanu —Asari Dokubo

Shaidu sun ce tankar na dauke da mai kimamin lita 33,000 a lokacin da da lamarin ya auku.

Wani ganau ya ce fashewar tankar ta yi ajalin mutum biyar a take yayin da wasu biyu suka samu raunuka.

Amma Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC) a yankin Idiroko, Akinwunmi Olaluwoye, ya ce mutum biyar ne.

Ya ce fashewar tankar ta mai da misalin karfe 8:15 na safiyar ranar Laraba ya kuma kona motoci da babura da dama.

Olaluwoye ya cewarsa tuni aka dauke gawarwakin wanda suka mutu zuwa ga iyalansu.

“Kafin mu karasa wajen direban tankar ya dauke kan motar, amma mun bar ’yan sanda suna gudanar da bincike,” a cewarsa.