✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin burodi ya yi tashin gwauron zabi a Edo

Farashin na burodi ya karu da sama da kashi 50 cikin 100.

Wani bincike ya nuna cewa farashin burodi ya yi tashin gwauron zabi da sama da kashi 50 cikin dari a Benin, babban birnin Jihar Edo. 

Binciken wanda da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya gudanar, ya gano cewa an samu karin farashin ne sakamakon karin farashin fulawa, wadda ita ce babbar sunadarin da ake amfani da ita wajen hada burodi.

A binciken da NAN ya yi, akwai yiyuwar farashin burodi zai ci gaba tashi a Najeriya nan da makonni masu zuwa.

Wannan ya faru ne sakamakon karancin alkama a duniya da masu bincike suka ce yakin da ake fafatawa tsakanin Rasha da Ukraine ne ya haddasa.

Binciken ya nuna a Benin ana sayar da karamin burodi kan farashin N120 a watan Nuwamba 2021, wanda a yanzu ake sayar da shi N180.

“Matsakaicin burodi da ake sayar da shi kan N300 watanni bakwai da suka wuce, yanzu ana sayar da shi a kan N450, yayin da babban burodi ake sayar da shi a kan N850, sabanin N500 da ake sayar da shi a watan Nuwamba 2021,” cewar wani mai sana’ar sayar da burodi.