✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Facebook da Instagram sun dakatar da shafukan Trump har ya sauka daga mulki

Mark Zuckerberg ya ce an dakatar da Donald Trump daga amfani da Facebook da Instagram har zuwa lokacin wa'adin mulkinsa.

Mamallakin kafofin sa da zumunta na Facebook da Instagram, Mark Zuckerberg, ya ce sun dakatar da shafukan Donald Trump har zuwa karshen wa’adin mulkinsa, a ranar 20 ga Janairu 2021.

Mark ya ce sun yanke shawarar daukar matakin ne sakamakon rikicin da magoya bayan Trump suka haifar a majalisar kasar Amurka.

A cewarsa, “Bayan tabbatar da wanda ya ci zabe, kwanaki 13 da suka rage, zamu yi amfani da su don tabbatar da zaman lafiya har zuwa lokacin da za a rantsar da sabon shugaban kasa.

“A shekarun da suka gabata, Trump ya sha karya dokokinmu, wajen wallafa abubuwan da ba su dace ba.

“Sai dai a wannan karon, abun ya zama na daban, saboda yana neman tada tarzoma.

“Mun san illar da zata biyo baya, idan muka kyale Trump yayi amfani da kafarmu wajen kawo hargitsi.

“Don haka mun dakatar da shafukansa na Facebook da Instagram, har sai bayan an yi rantsuwa,” in ji Zuckerberg.

Hamshakin mai kudin, ya ce shekarun da suka wuce, an kyale Trump ya yi abin da ya gama, amma a wannan karon ba za a kyale shi ba, saboda zai iya haifar da fitina.