✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EURO 2020: Fitattun ’yan kwallo 6 da ba sa buga Gasar Nahiyar Turai a bana

A ranar Juma’a ce aka fara gasar cin Kofin Nahiyar Turai, mai taken EURO 2020 wanda annobar Coronavirus ta hana a buga bara, inda kasashe…

A ranar Juma’a ce aka fara gasar cin Kofin Nahiyar Turai, mai taken EURO 2020 wanda annobar Coronavirus ta hana a buga bara, inda kasashe 24 za su fafata a gasar.

Kasar Portugal ce ke rike da kofin, inda ta doke kasar Faransa a wasan karshe da aka buga a kasar Faransa a shekarar 2016.

Sai dai a daidai lokacin da ake murnar fara gasar, wadansu suna alhinin ’yan wasansu ba za su buga gasar ba.

Aminiya ta rairayo wadansu fitattun ’yan wasa da ba za su buga gasar ba da suka hada da:

Sergio Ramos

Sergio Ramos

Babba daga cikin fitattun ’yan wasan da babu su a gasar, shi ne Sergio Ramos, dan wasan Real Madrid da Spain mai shekara 35.

An yi mamakin ganin yadda kocin Spain Luis Enrique, wanda tsohon kocin Barcelona ne ya ki gayyatar dan wasan, duk da cewa har yanzu yana tashe duk da shekarunsa sun ja da kuma raunuka da yake fama da su.

Erling Haaland

Erling Haaland

Erling Haaland matashin dan wasa ne da tauraronsa ke matukar haskawa a yanzu.

Dan wasan mai shekara 20 dan wasan kasar Norway ne da Dortmund.

Yana cikin ’yan wasa masu matukar daraja a duniyar kwallo a yau, domin manyan kungiyoyin kwallon kafa suna zawarcinsa.

Za a iya cewa shi ne dan wasan da ke tsakiyar ganiyarsa da ba ya buga gasar ba saboda kasarsa ta Norway ba ta samu zuwa gasar ba.

Zlatan Ibrahimovic

 

Zlatan Ibrahimovic

Dan wasan kasar Sweden mai shekara 39, an sanar da cewa zai dawo taka leda ga kasarsa ta Sweden bayan ya yi ritaya da kusan shekara biyar, sai dai rauni ya hana shi zuwa gasar.

Virgil van Dijk

Virgil van Dijk

Fitaccen dan wasan baya na Liverpool ne wanda shi ma kwallon kafa ke yi da shi a wannan zamani.

Dan wasan kasar Netherlands ne mai shekara 29. Sai dai shi ma yana fama da jinya a yanzu wanda ke nufin ba zai buga gasar ba kasancewar bai gama warwarewa ba daga jinyar da yake yi ba.

Jan Oblak

Jan Oblak

Jan Oblak fitaccen mai tsaron gida ne da shi ma yake zamani a Kungiyar Atletico Madrid.

Dan wasan kasar Slovenia ne mai shekara 28 wanda shi ma bai samu zuwa gasar ba saboda kasarsa ba ta samu gurbi a gasar ba.

Miralem Pjanic

Miralem Pjanic

Dan wasan Barcelona bai samu zuwa gasar ba saboda kasarsa ta Bosnia ba ta samu shiga gasar ba.