✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: Ministoci da gwamnonin Kudu sun ziyarci Legas

Sun alakanta ibtila'in da wani shiryayyen lamari da aka kitsa domin karya tattalin arzikin jihar.

A ranar Lahadi 25 ga watan Oktoban 2020 ne Ministoci da Gwamnonin yankin Kudu maso Yamma suka ziyarci Jihar Legas domin jajanta wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu kan dimbin asarar da zanga-zangar #EndSARS ta haifar a jihar.

Bayan da suka kewaya don gane wa idanunsu irin barnar da ta biyo bayan kone-konen, shugabannin sun yi zargin wani shiryayyen lamari ne da aka kitsa domin karya tattalin arzikin jihar Legas.

Wanda ya yi magana a madadinsu, Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ya bayyana haka a lokacin ziyarar tasu.

Aminiya ta kawo maku hotunan ziyarar jajen da kuma gani da ido da shugabannin yankin suka kai jihar Legas.