✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda jawabin Buhari kan #EndSARS ya tayar da kura

Yabo da kushe sun dabaibaye jawabin Shugaba Muhammadu Buhari kan #EndSARS

A yammacin ranar Alhamis ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga al’ummar Najeriya, kan tashin-tashina da aka samu sakamakon zanga-zangar #EndSARS.

A jawabinsa, Buhari ya ja hankalin matasan kasar da su kauce wa fadawa tarkon bata-gari da ke neman amfani da su wajen ta da hankulan jama’a.

Sai dai Aminiya ta gano cewa matasa da dama ba su ji dadin shugaban kasar ba, musamman ganin yadda al’amura suka rincabe a kasar cikin makonni biyu da suka shude.

Jim kadan bayan jawabin nasa, matasa da dama suka fara yin tsokaci musamman a shafukan zumunta.

Wasu na ganin jawabin da Shugaba Buhari ya yi ba komai ba ne, face bata lokacin mutane saboda a ganinsu, ba shi da wani amfani balle tasiri.

Wasu kuma na ganin cewa shugaban bai bawa mutanen da suka rasa rayukansu a Lekki, Jihar Legas muhimmanci ba, duba da yadda ya gama jawabin nasa ba tare da ya jajantawa iyalansu ba.

Har wa yau, wasu na cewa kamata ya yi ya mai da hankali wajen kawo karshen yajin-aikin malaman jami’o’i da kuma rage wa mutane talauci da suke ciki ta hanyar rage kudin wuta da farashin Man fetur.

Daga wani bangaren kuwa, wasu matasan na ganin shugaban kamata ya yi ya mai da hankali wajen kawo karshen tsadar kayan masarufi da ke kawo tsananin rayuwa a mulkin nasa.

Daga cikin wanda suka bayyana ra’ayinsu a kafar sadarwa ta Facebook akwai; Aisha Umar inda ta ce “Wallahi na yi mamakin rashin yin maganar kisan Zamfara, wallahi abun Allah wadai ne”.

Wasu sun tofa albarkacin bakinsu game da jawabin na shugaban kasa.

Eleni Giokos ta ce “Abun mamaki ya gama jawabi gaba daya bai ambaci kisan da aka yi a Lekki ba”.

Amma Amin Sulaiman ya ce, “Hakika ya yi magana game da jami’an tsaron da aka yi wa kisan gilla kuma abin alhini ne yadda aka nuna musu rashin imani”.

Splendour ta ce “Ubangiji ka kawo mana dauki, wannan kasa tamu ta shiga hannun azzaluman shugabanni”.

Musa Muhammad Dambatta ya ce, “Jawabin ya yi kyau. Da fatan za a dakatar da zanga-zangar domin gwamnati ta yi abin da ya kamata”.

Emmanuel Omaram ya ce “Shugaba Buhari ya kamata ka yi amfani da nagartar da kake da ita domin kawo aminci da daidaituwan al’amura a Najeriya”.

A jawabin nasa shugaba Buhari ya bayyana cewa babu wata gwamnati da ta taba yunkuri irin tasa wajen cire mutane daga kangin talauci.

Buhari ya bayyana cewa daga cikin tsare-tsaren da gwamnatinsa ta fito da su akwai shirin:

  • Farmermoni
  • Tradermoni
  • Marketmoni
  • N-Power
  • N-Tech da kuma
  • N-Agro

Sai dai wadannan shirye-shirye da Gwamnatin Tarayya ta fito da su domin cire mutane daga talauci, wasu na ganin ba za su gamsar yadda ya kamata ba.