✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EndSARS: Gwamnatin Filato ta sassauta dokar hana fita

Gwamnatin Jihar Filato ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta sanya sakamakon rikicin da ya barke a jihar a zanga-zangar #EndSARS. Sakataren…

Gwamnatin Jihar Filato ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta sanya sakamakon rikicin da ya barke a jihar a zanga-zangar #EndSARS.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Danladi Attu ya ce gwamnatin jihar ta dauki mataki ne bayan taron masu ruwa da tsaki da Gwamna Simon Lalong ya jagoranta.

Ya ce a taron ya amince a sassau dokar daga awa 24 ta koma daga karfe 6 na safe zuwa 8 na dare, a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da abin ya shafa.

Sassaucin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a saboda ganin hankula sun kwanta a wadannan wurare.

Gwamnatin jihar ta kuma haramta kowace irin zanga-zanga a kokarinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.