✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufa’i ya mika wa sabon Sarkin Lere sandar girma

El-Rufa'i ya ce ba ya son ya ga ’ya’yan sarki sun zauna ba sa komai sai jiran sarauta.

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya mika wa sabon Sarkin Lere, Injiniya Sulieman Umaru sandar girma yau Laraba a garin Lere na Jihar Kaduna.

Sarkin Lere na 14 ya karbi sandar girman ce bayan rasuwar tsohon sarkin masarautar, marigayi Birgediya Janar Garba Muhammed, a watan Afrilun da ya gabata.

Da yake jawabi a taron mika sandar, El-Rufa’i ya bayyana cewa irin sabon Sarkin ake bukata wanda ya fita waje, ya yi  aiki ya sami gogewa ya kuma kware wajen taimakawa jama’a.

Ya ce “bama son mu ga ’ya’yan sarki sun zauna ba sa komai sai jiran sarauta.

El-Rufai a lokacin da yake mika wa sabon sarkin sandar girma

Muna son ganin ’ya’yan Sarakuna suna fita waje su samu gogewa a aikin gwamnati da kasuwanci da taimakawa jama’a da masarautarsu kafin Allah ya ba su sarauta.

“Duk Sarakunan da muka nada a Jihar Kaduna, sai mun duba mun ga cewa suna da ilmi da gogewa a aiki da shugabanci, kuma sun nuna cewa su adalai ne a ayyukan da suka yi a baya.’’.

Ya yi  kira ga Sabon Sarkin da ya tashi tsaye ya yi aiki kamar yadda mahaifansa, marigayi Mai martaba Alhaji Muhammed Umar Lere da marigayi Birgediya Garba Muhammed Lere suka yi.

Kazalika, ya roki al’ummar masarautar da su bai wa sabon Sarkin goyon baya domin ya ci gaba da aikin da ya gada daga iyayensa.

Gwamna El-Rufa’i ya yi bayanin cewa alkawarin da aka yi na gina jami’a a masarautar yana nan kuma yana sa ran cikin yardar Allah za a fara ikin kafin ya sauka daga mulki.

A nasa jawabin, sabon Sarkin ya mika godiyarsa ga gwamna El-Rufai kan wannan dama da ya bashi na dorawa kan abubuwan da iyayensa da kakanninsa suka yi.

Ya bai wa gwamnan tabbacin cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen sauke wannan nauyi da rataya a wuyansa

Aminiya ta ruwaito cewa, taron ya sami halartar manyan Sarakuna daga ciki da wajen Jihar Kaduna da suka hada da Mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, da Sarkin Nasarawa Mai martaba Alhaji Ibrahim Usman Jibrin.

Akwai kuma ’yan siyasa da suka halarci taron da hada da Sanata Sulieman Abdu Kwari da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Honarabul Alhassan Ado Doguwa da dan majalisar mai wakiltar mazabar Lere a Tarayya, Injiniya Ahmed Manir da sauransu.