✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta karbe gidaje 324 a Kano

Ana zargi an gina gidajen ne da kudin Hukumar Kula da ’Yan Fansho.

Hukumar da ke Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa ta’annati, EFCC, ta ce wata kotu ta ba ta damar karbe gidaje 324 a Jihar Kano da ake zargi an gina ta hanyar amfani da kudaden haramun.

Da yake magana bayan yanke hukuncin a wannan Larabar, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce galibin kadarorin na nan a wasu yankuna masu tsada da ke birnin Dabo.

A cewarsa, Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, “ya bayar da umarni a karbe” gidajen kamar yadda EFCC ta bukata a wajensa.

Hukumar ta ce gidajen sun hada da guda 168 da ke Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Bandirawo City; guda 122 da ke Sheikh Nasiru Kabara (Amana City), Kano da kuma 38 da ke Sheikh Khalifa Ishaq Rabiu City, Kano.

EFCC ta kara da cewa gidajen sun hada da masu dakuna biyar-biyar, hurdudu, uku-uku da masu biyu-biyu da sauransu.

A cewarta, ana zargi an gina gidajen ne da “kudin da aka samu ta hanyar haramun daga Hukumar Kula da ’Yan Fansho ta Jihar Kano.”