✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ECOWAS ta sanar da lokacin fara amfani da kudin bai-daya

An sanya lokacin da Kasashen Yammacin Afirka za su fara amfani da ECO.

Shugabannin Kungiyar Raya Tattalin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) sun sun cimma matsaya a ranar Asabar kan fara amfani da kudaden bai daya a shekarar 2027.

Tun a bara waccan kasashen ECOWAS suka aminta tare da yi wa kudi na bai-daya lakabi da sunan ‘ECO’ tare da shirya fara amfani da shi a shekarar 2020, amma bullar annobar COVID-19 ta kawo musu cikas.

  1. Ta watsar da aikin sakatariya domin gyaran takalmi
  2. IPOB ta kulla kawance da ’yan tawayen Kamaru

Sanarwar da ECOWAS ta bayar, ta ce za a samar da kudaden a shekara mai zuwa, sannan kasashen da suka cika ka’ida za su iya amfani da kudaden.

Shugabannin sun cimma yarjejeniyar yayin wani zama da suka yi a watan Yunin 2019 a Abuja, Najeriya.

Taron ya kuma bai wa cibiyar hada-hadar kudaden yammacin Afirka da kuma manyan bankunan kasashen yankin umarnin soma aikin aiwatar da shirin fara amfani da kudin na bai-daya kamar yadda aka tsara.

Tunanin samar da kudin bai-daya ga kasashen Afirka ta yamma ya samo asali ne kusan shekaru 30 da suka gabata, da zummar bunkasa kasuwanci da kuma ci gaban tattalin arzikin yankin.