✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ECOWAS ta dakatar da Burkina Faso saboda juyin mulkin sojoji

Matakin na ECOWAS ya sa kasar ta zama ta uku da aka dauki matakin dakatarwar a kanta cikin wata 18.

Kungiyar Cinikayyar Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta dakatar da Burkina Faso daga cikinta saboda juyin mulkin da sojojin kasar suka yi.

A makon da ya gabata ne dai sojojin suka yi wa Shugaba Christian Kabore a juyin mulki, tare da tsare shi, shi da wasu mukarraban gwamnatinsa.

Matakin na ECOWAS ya sa kasar ta zama ta uku da aka dauki matakin dakatarwar a kanta cikin wata 18 saboda juyin mulkin.

Sanarwar dakatarwar na zuwa ne bayan sojojin kasar sun kwace mulki daga hannun Gwamnatin farar hula ta kasar, saboda yadda suka ce tana fuskantar barazana daga kungiyoyi masu dauke da makamai.

Sun dai zargi gwamnatin da kin yin wani katabus kan rigingimun da suke ta kara ta’azzara a fadin kasar, wadanda suka yi sanadiyar rasa ran dubban mutane.

Shugabannin kasashen yankin dai sun hadu ne yayin wata tattaunawa ta intanet ranar Juma’a, kuma ana sa ran nan da ’yan kwanaki masu zuwa su aike da wata tawagar jakadu zuwa Ouagadougou babban birnin kasar.

Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, wanda shi ne Shugaban ECOWAS mai ci, ya kwatanta juyin mulkin da wani yunkurin yin karan tsaye ga tsarin dimokuradiyya.

“Duniya tana kallonmu don ta ga matakin da za mu dauka a kan wannan lamarin,” inji shi.

Yayin taron dai, wanda aka shafe kusan sa’o’i uku ana tattaunawa, Shugabannin sun yi kira da a gaggauta sako Shugaba Kabore da sauran jami’an gwamnatinsa da aka tsare.