✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ECOWAS ta cire takunkumin da ta kakaba wa Mali

Za kuma a bude iyakokin kasar da na makwabtanta

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta cire takunkumin da ta sanya wa kasar Mali bayan sojojin da ke mulkin kasar sun yi tayin mika mulki cikin shekara biyu masu zuwa.

Kungiyar dai ta kakaba wa Mali takunkumin ne a watan Janairu bayan gwamnatin mulkin sojin kasar ta ce ba za ta shirya zabe ba a cikin wata daya kamar yadda aka tsara tun da farko.

Shugaban kungiyar ta ECOWAS, Jean Claude Kassi Brou, ya shaida wa wani taron manema labarai ranar Lahadi cewa za a dage takunkumin ne ba tare da wani bata lokaci ba.

Kazalika, ya ce za a bude iyakokin kasar ta Mali da makwabtanta, yayin da ma’aikatan ofisoshin jakadanci za su sake komawa birnin Bamako nan ba da jimawa ba.

“Sai dai Shugabannin kasashen yankin sun amince a ci gaba da amfani da takunkuman da daidaikun kasashensu suka saka mata da kuma dakatarwar da suka yi mata daga kungiyar, har sai ta koma kan tafarkin Dimokuradiyya,” inji Jean Claude.

Jerin takunkuman dai sun yi matukar kassara tattalin arzikin kasar yayin da rayuwar mutanen kasar ta dada shiga kunci.

Mai shiga tsakani na kungiyar, kuma tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ziyarci kasar a makon da ya wuce, inda daya daga cikin ’yan tawagarsa ya ce ana samun ci gaba.