✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dusar kankara ta tsayar da al’amura cak a birnin Istanbul na Turkiyya

Gwamnati dai ta umarci mutane da su zauna a gida, saboda dusar za ta karu.

Hukumomin kasar Turkiyya sun aike da dakaru na musamman domin su share manyan hanyoyin da dusar kankarar ta mamaye sannan ta tsayar al’amura cak a birnin Istanbul na kasar.

Rahotanni sun ce gwamnati ta kuma ba da umarnin yin amfani da jiragen sojoji wajen yin jigilar wadanda suka kwanta rashin lafiya zuwa asibiti.

Dusar kankarar dai wacce ba kasafai ake ganin irinta ba, ta tsayar da kusan ilahirin harkokin sufuri a birnin, wanda yake zama mafi girma a kasar.

Kazalika, gwamnatin ta kuma haramta yin amfani da babura masu kafa biyu ranar Litinin, daga bisani kuma ta haramta motocin da ba na haya ba a ranar Talata.

An kuma rurrufe makarantu da manyan shaguna sannan aka umarci mutane su zauna a gida, saboda an yi harsashen dusar zata ci gaba da karuwa a ’yan kwanaki masu zuwa.

A cewar Magajin Garin Istanbul, Ekrem Imamoglu, “Babban abin shi ne mutanenmu su takaita fita waje matukar ba ta zama dole ba saboda yanayin da ake ciki.

“Akwai yankunan da dusar ta kai kaurin kusan santimita 80 (kafa 2.6) a sassa da dama ma birnin,” inji shi.

Manyan hanyoyin birnin dai ciki har da wacce take zuwa babban filin jirgin sama, da wacce take tafiya zuwa babban birnin kasar na Ankara, duk an rufe su a daren Litinin.

Gwamnan birnin na Istanbul dai ya ce an bude masallatai 71 domin su zama matsugunai na wucin gadi ga mutanen da ababen hawansu suka makale a kan hanyoyin birnin.

Yanayin ya kuma tilasta dakatar da zirga-zirgar jirage zuwa wajen birnin daga ranar Litinin, filin da yana daya daga cikin wadanda suka fi yawan sauka da tashin jirage a duniya.