✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta gayyaci ‘yan majalisar Neja kan shirya zanga-zanga

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta gayyaci wasu mambobin Majlisar Dokoki ta Jihar Neja guda biyu

Hukumar Tsaro ta DSS ta gayyaci wasu mambobin Majlisar Dokoki ta Jihar Neja guda biyu bisa zarginsu da hannu a kokarin shirya zanga-zanga kan matsalar wutar lantarkin da ta addabi jihar.

‘Yan majalisun da aka gayyata sun hada da Malik Madaki Bosso wanda shine shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kwadago da ingantuwar ayyuka da kuma Injiniya Mohammed Haruna dan majalisa mai wakiltar mazabar Bida ta biyu, mamba a kwamitin kuma shugaban kwamitin matasa na majalisar.

Hukumar dai ta umarci ‘yan majalisar da su bayyana a wani ofishin ‘yan sanda ranar Laraba da misalin karfe 10 na safe.

Da yake jawabi ga ‘yan jarida a kan gayyatar, Injiniya Haruna ya ce DSS ta gayyace su ne ta hanyar aike musu da sammaci ta hannun akawun majalisar saboda dagewarsu kan hada gwiwa da wasu masu kishin kasa a jihar don ganin sun sami wadatacciyar wutar daga Kamfanin Rarraba Hasken Lantarki na Abuja (AEDC).

Ya ce karancin wutar da ake samu daga kamfanin a jihar shine ya jawo hankalin zauren majalisar, wanda bayan tattaunawa ya amince da kafa kwamitin da zai tilasta inganta samuwar wutar.

Sai dai dan majalisar ya sha alwashin cewa gayyatar ba za ta sare musu gwiwa ba kan barazanar da suka yi ta rufe madatsun ruwan da ake amfani da su a jihar matukar ba a sami ingantuwarta ba da akalla sa’o’i 20.