✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta gayyaci Fani-Kayode saboda kalamansa kan yunkurin juyin mulki

Ya ce an aike masa da takardar gayyatar, kuma zai je da safiyar Litinin

Hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci jigo a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode saboda kalaman da ya yi cewa ana yunkurin yin juyin mulki a Najeriya.

Femi, wanda tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama ne a Najeriya ya tabbatar da gayyatar a wata sanarwa da ya wallafa da safiyar Litinin.

Sai dai ya ce zai amsa gayyatar saboda ba ya jin tsoron komai kuma zai ci gaba da bayyana ra’ayinsa matukar yana numfashi.

Ya ce, “Kwanaki uku da suka wuce, lokacin da na wallafa wani sako a shafin Twitter kan wani rahoto da ke cewa Atiku na tattaunawar sirri da wasu Janar-Janar na soja, sai wani jami’in DSS ya aiko min da rubutaccen sako cewa suna gayyata ta saboda dalilan tsaron kasa.

“Amma na yi watsi da sakon saboda ba ni da tabbaci kan sahihancinsa. Ba inda zan je sai an gayyace ni a hukumance.

“Cikin mamaki sai ga shi an sake aiko min da wasikar bayan kwana biyu, ana shawarta ta da na bayyana a ofishinsu, kuma na dauki batun da muhimmanci ko kuma rai ya baci.

“Idan da ba don ain riga an aike min wancan sako tun kwana uku da suka wuce ba, da sai in ce maganar da Atiku ya yi ce ta sa aka gayyace ni. Na zaci suna amfani ne da maganar da karnukan farautar dan takarar da ya fara jiyo kamshin faduwa ya yi.

“Yanzu dai ta tabbata ba maganar Atiku suke bi ba, suna kokarin yin aikinsu ne bisa doron doka a kokarinsu na yin cikakken bincike.

“A kodayaushe suka gayyace ni, nakan amsa, yanzu ma kuma zan je da safiyar Litinin,” in ji shi.

A wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafin Twitter ranar Asabar, Fani-Kayode ya yi zargin cewa Atiku na tattaunawa da manyan sojojin a sirrance.

Sai dai tuni hedkwatar tsaro ta kasa ta karyata zargin na Fani-Kayode, inda ta jaddada amannar da ta yi da tsarin mulkin Dimokuradiyya.