✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darussa uku da Najeriya ka iya koya daga annobar coronavirus

Annobar coronavirus ta yi wa kasashe da dama ba-zata kasancewar ba su shirya tunkararta; hakan ne ma ya sa wasu manyan kasashe suka ma suka…

Annobar coronavirus ta yi wa kasashe da dama ba-zata kasancewar ba su shirya tunkararta; hakan ne ma ya sa wasu manyan kasashe suka ma suka gigita, balle kasashe masu masu tasowa irin Najeriya.

To ko wadanne darussa Najeriyar za ta iya koya daga wannan annoba.

Aminiya ta tambayi wasu masana uku a bangarorin yaruwa daban-daban, ko wadanne muhimman darussa uku ko wannensu yake ganin Najeriya za ta iya koya?

Idayat Hassan, mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum

1. Lafiya uwar jiki: 

Abu na farko shi ne Najeriya ta fara lura da bangaren lafiya. Saboda bangaren lafiya na da alaka da siyasa da tattalin arzikin kasa. Ya zama dole kasa ta san muhimmancin harkar lafiya.

2. Shirin zaune ya fi na tsaye:

Akwai bukatar tsare-tsaren tattalin arzikin kasa, ba wai kirkirar cibiyoyi ba kawai. Abu ne da ya shafi yadda ake gudanar da tsare-tsaren a matsayin kasa mai zaman kanta. Duk da yake Najeriya ta yi kokari, amma da a ce an shirya tsarin da kyau da abin ya fi haka. Idan aka cire tsarin tattalin arzikin kasa an cire abu muhimmi.

3. Abokin kuka, ba a boye masa mutuwa:

Idan muka duba tsakanin shugabanni da wadanda ake mulka, akwai rashin yarda da juna. Wasu da yawa ba su yarda da tsarin wannan gwamnatin ba balle su bayar da goyon baya ga shugabanni. Yana da kyau a fahimci dangantakar da take tsakanin ’yan kasa da shugabanni. Idan da akwai fahimtar juna da gwamnatin Najeriya za ta yi fiye abin da take yi a yanzu.

Dokta Isa Abdullahi, Malami a Sashen Nazarin Tattalin Arziki na Jami’ar Tarayya da ke Kashere a jihar Gombe

1. Ajiya maganin wata rana:

Kasashen da suka ci gaba duk lokacin da suka samu dama suka ga rarar wani abu na dukiya, suna kokarin su ga sun ajiye sun gina kasar, sun inganta rayuwar talakawan kasar, sannan kuma su ajiye wani abu ta yadda idan wani hali irin wannan ya taso na rashin dadi za su yi amfani da shi wajen harkokin inganta kasar su. Wajibi ne Najeriya ta yi koyi domin yanzu a halin da ake ciki inda farashin mai ya yi kasa, idan ba taimako aka samu daga wani wuri ba, karshenta wasu jihohin ma ba za su iya biyan albashi ba.

2. Gida biyu maganin gobara:

Mun dade da yin watsi da bangaren da ya shafi noma da ma’adanai da sauran muhimman abubuwan da za su iya kawo wa kasar arziki. Hanyar samun kudin shiga daya ce kawai, da wani abu ya shafe ta za mu shiga matsaloli a kan komai. Yanzu ga wani abu da yake kunno kai ma, muna addu’ar Allah Ya sa coronavirus ta wuce, [amma] matsalar da tattalin arzikin kasa ke fuskanta a yanzu ita ce kullum Turai da Amurka, wadanda su ke sayen man, ba sa son motoci masu amfani da fetur da diesel, suna ta kokarin kawo motocin da za su yi amfani da wutar lantarki da hasken rana (solar) da sauransu. A Najeriya ko tunanin haka ba ma yi. Saboda haka mu koyi darasi.

3. Don gobe ake wanke tukunya:

Wajibi ne a samar da ayyukan yi a kasa. Tun makon farko zuwa na biyu ake cewa an kiyasta za a yi asarar Naira biliyan 160. Misali a bangaren sufuri na jiragen sama, wasu sun ce za su iya biyan rabin albashi na watan Afrilu wasu sun ce kwatata ba za su iya biya ba, saboda ba su yi wani cinikin da za su iya biyan kudaden ba. An kiyasta sama da mutum 20,000 zuwa 30,000 a wannan bangaren za su rasa ayyukansu.

Gyara:

Kowa ya debo da zafi…:

Wani karin darasin shi ne, shugabannin Afirka da suke sace kudade, lokaci zai zo ba za su iya tsallakawa Turai da Amurka don su adana dukiyar da suka sata ba.

Dokta Nasir Sani Gwarzo, Masanin kiwon lafiyar al’umma kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu ta Tarayya

1. Kowa ya ce zai ba ka riga…:

Wannan annobar ta tona asirin bangaren kiwon lafiya. Abu ne sananne, amma ta kara bayyana shi a fili, cewa lallai harkar kiwon lafiya a Najeriya ba ta kai matakin da ake bukata ba. Wato akwai bukatar karin gyara a tsarin kiwon lafiya, tun daga kayan asibitocin da tanadin su, da kuma yawan ma’aikatan kiwon lafiyar musamman likitoci da kuma bangaren gwajegwaje.

2. Rashin sani ya fi dare duhu:  

Ita wannan annoba a kasashen da suka ci gaba, gabanin barnar ta bayyana ake yi wa mutane bayani, cewa idan an kai mataki kaza ga sabuwar dokar da za a fito da ita, saboda haka idan an kai wannan matakin sai ka ga mutane a shirye suke. Amma a Najeriya sai ka ga ana tare mutane ana hana su fita, wani bai san me ya sa aka hana mutane fitar ba, da sun fahimta da su ma sun ba da tasu gudunmawar. A China suna ganin cewa rashin fitar da kowa yake yi wata gudunmawa ce ta taimaka wa al’umma da kuma kare kai daga cutar. A Najeriya kuwa wani gani yake shi an takura masa an cuce shi an hana shi fita.

3. Ba a fafe gora ranar tafiya: 

Idan a Turai za a tattare mutane a ce kowa ya zauna a gida, to mutane na da karfin arzikin da za su yi abinci, wani ma ya yi wata bai fito ba. Amma a nan zai yi wuya mutum ya yi wata guda bai fito ba. Saboda idan ma yana da kudin ba wutar lantarki da za ta iya taimaka masa ya ajiye abincin a freezer don kar ya lalace, idan kuma bai da kudin sai ya fita ya nemo. Mafi yawan mutanenmu sai sun fita suke samun abin da za a ci tare da iyali, idan mutum bai fita ba, a ina zai samu?

Gyara:

Kayan aro ba ya rufe katara:

A bangaren masana’antun harhada magunguna mun gane kuskuren mu, wanda mu mutanen Najeriya ba mu farga ba. Misali, Najeriya ta dogara da kasashe biyu wajen samun kayan hada magunguna. Kwanan da aka fara wannan annoba da China da Indiya—a nan muka saba sayowa, sannan mu zo mu hada magungunan mu a Najeriya—sun kafa doka sun daina sayarwa har sai annobar ta wuce. Hakan ya sa yanzu muka shiga taskun ina za mu je mu sayo wadannan kayan hada magungunan? Don haka Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu ta fara tunanin cewa da zarar wannan annobar ta wuce a fara tunanin kirkirar irin namu masana’antun a cikin gida, yadda koda al’amari ya baci wata kasa ba za ta yi mana yanga ba.