✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daruruwan ’yan sanda sun karya doka —Rahoto

Rahoton ya samu wani dan sanda daya da ya aikata ba daidai ba har sau 11.

Wani sabon rahoton kan halayen ’yan sandan Landan ya gano daruruwansu suna karya doka da ka’idojin aikin dan sanda.

Rahoton ya binciki ’yan sandan Birni ne – ’yan sandan da suke kula da Birnin Landan, inda ya samu shaidun nuna bambancin launin fata da kyama ga mata da kuma nuna bambancin jinsin da rashin ladabi a tsakaninsu.

Kwamishinan ’Yan sandan Birnin Landan, Sa Mark Rowley – ya ce kamata ya yi a ce an kori daruruwan ’yan sandan.

Bincike kan yadda ’yan sandan suke gudanar da aiki an kaddamar da shi ne bayan an samu wani dan sandan Birnin Landan da laifin kisan wata mata mai suna Sarah Everard a watan Maris din bara.

An bai wa Baroness Louise Casey alhakin tattara rahoton wuri daya tare da duba adadin ’yan sandan da keta ka’idoji da kuma dokoki.

Ta gano daruruwan ’yan sanda sun karya doka da ka’idojin aikin dan sanda, inda ta ba hukumar ’yan sandan Birnin Landan jerin wuraren da ake bukatar su inganta aikinsu.

Rahoton ya samu wani dan sanda daya da ya aikata ba daidai ba har sau 11.

Kuma Baroness Louise Casey ta rubuta yadda ake nuna bambancin launin fata da na jinsi hatta ga ’yan sanda bakaken fata da ’yan asalin Asiya.

’Yan sandan kuma kan bambance tsakanin mata da maza wajen hukunta su, ko su tauye matan ko su ki ba su dama saboda jinsinsu.

Sannan ’yan sandan Birnin Landan din sun ci gaba da nuna fiffiko ga jami’ansu fararen fata a kan bakaken fata ko ’yan Asiya.

Kuma hakan na faruwa ne a daukacin Birnin Landan.

Magajin Garin Birnin Landan, Sadik Khan ya ce, rahoton yana nuna cewa ’yan sandan Birnin Landan “ba su cancanci aikin da aka ba su ba,” wanda hakan ke nufin akwai bukatar a samu babban sauyi.

Sakatariyar Harkokin Cikin Gidan Birtaniya, Misis Suella Brabeman, ta ce “wajibi ne su gyara halayensu.”

Ana sa ra Baroness Louise Casey ta fadada tare da mika cikakken rahotonta nan gaba kadan.