✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Najeriya ya lashe zaben dan majalisa a Amurka

Dan asalin Najeriya ya zama dan majalisa mai wakiltar gundumar Columbia a kasar Amurka

Wani matashi dan asalin Najeriya Oye Owolewa ya zama dan majalisa mai wakiltar gundumar Columbiya a kasar Amurka bayan ya lashe zabe a karkashin jam’iyyar Democrat.

Mista Oye dai ya sami kaso 82.65 cikin 100 wanda ya kai kuri’u 135,234  inda ya kayar da abokin karawarsa Joyce Robinson-Paul wanda ya sami kuri’u 15,541 kacal.

Matashin, mai kimanin shekara 30 dan asalin yankin Omu-Aran ne a Jihar Kwara.

Yana daya daga cikin ’yan asalin Najeriya guda tara da suka tsaya takara a zaben na kasar Amurka.

Ya kammala karatun digirin digir-gir dinsa a fannin Kimiyyar Harhada Magunguna daga Jami’ar Norteastern da ke birnin Boston a kasar ta Amurka.

Tuni dai ’yan Najeriya da dama suka fara mika sakon fatan alheri da taya murna ga Mista Oye, ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Kwara, inda matashin ya fito kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba, Saraki ya ce nasarar wata ’yar manuniya ce kan cewa matasan Najeriya za su iya cimma manyan burikansu a rayuwa.