Shaharren dan gudun hijirar nan, dan kasar Ethiopia mai suna Haile Gebre Selassie ya yanke shawarar yin takatar kujerar dan majalisa a shekarar 2015 idan Allah Ya kaimu.
dan kimanin shekara 40, Haile ya bayyana haka ne bayan rade-radin da aka dade ana yi cewa dan tseren ya kusa yin ritaya daga yin tsere.
Sai dai rahotannin da aka samu ba su ambaci jam’iyyar da dan tseren zai yi takara a kan ta ba
Majalisar dokokin Ethiopia tana mamaye ne da ’yan jam’iyyar Ethiopian Poeple’s Rebolutionary Democratic Front (EPRDF). Majalisar na dauke ne da mutum daya tilo wanda ya fito daga wata jam’iyya daban.
“Na samu sakonnin fatan alherin na neman tsayawata takara daga masoyana masu dinbin yawa don haka na yanke wannan shawara”, inji Haile.
Haile ne dan tseren da ya taba lashe lambobin Zinare har sau hudu a gasar tseren olamfik ta mita dubu 10 da aka yi a shekarar 1996 da kuma 2000.
A shekarar 2010 ne ya bayar da sanarwar yin ritaya bayan ya samu rauni amma bayan da ya samu sauki ne ya sake komawa ruwa.
A watan Afrilun wannan shekara ce dan tseren ya lashe gudun fanfalakin da aka yi a bienna. Ya halarci gasar tseren da aka yi a Boston da ke Amurka inda wasu ’yan ta’adda suka dasa bom da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku.
Jam’iyyar EPRDF ta Ethiopia dai ana zarginta da mulkin danniya. Tana amfani da karfin iko wajen murkushe ’yan adawa musamman wajen garkame masu tsattsauran ra’ayi da ’yan jarida.
Dan gudun fanfalakin Ethiopia Haile Gebre Selassie zai koma harkokin siyasa
Shaharren dan gudun hijirar nan, dan kasar Ethiopia mai suna Haile Gebre Selassie ya yanke shawarar yin takatar kujerar dan majalisa a shekarar 2015 idan…
