✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan bindiga ya kashe mutum 13, ya jikkata 20 a makarantar firamare a Rasha

Wani dan bindiga ya harbe mutum 13 har lahira tare da jikkata wasu kusan 20 a wata makarantar firamre a kasar Rasha.

Wani dan bindiga ya harbe mutum 13 har lahira tare da jikkata wasu kusan 20 a wata makarantar firamre a kasar Rasha.

Hukumomin kasar sun ce a safiyar Litinin ne maharin, wanda ba a san ko wane ne ba, ya hallaka jami’an tsaro biyu da dalibai biyar da malamai biyu da wasu mutane a makarantar da ke yankin Izhevsk.

Kwamitin binciken da gwamnatin Rasha ta kafa ya ce ’yan shekara biyar zuwa 11 ne ke karatu a makarantar da maharin ya kai wa farmakin dauke da makamai biyu a Lardin Udmurtia mai nisan kilomita 960 daga Moscow, babban birnin kasar.

Gwamnan Lardin Udmurtia, Alexander Brechalov, ya ce dan bindigar, ya harbe kansa bayan harin, kuma tuni aka kwashe daukacin mutanen da ke makarantar tare da killace ta.

Har yanzu babu karin bayani game da dan bindigar ko makasudin harin nasa.